Iran Ta Ritsa Sojojin Amurka Suna Barci bayan Sace Mata Jiragen Ruwa
- Rundunar sojin ruwan Iran ta yi ikirarin cewa ta kwato jiragen dakon man fetur guda biyu da take zargin sojojin Amurka sun kwace
- Kwamandan rundunar sojin ruwan Iran, Shahram Irani, ya ce dakarunsu sun shiga jiragen ne lokacin da ma’aikatan jirgin suke barci, suka karɓe su
- Sai dai rundunar sojin Amurka ta musanta ikirarin, tana mai cewa babu gaskiya a zargin, kuma Iran ba ta da rundunar sojin ruwa a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran – Rundunar sojin ruwan Iran ta yi ikirarin cewa ta kwato jiragen dakon man fetur guda biyu da ta ce sojojin Amurka sun sace, lamarin da ya ƙara tayar da muhawara kan rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Rahoto ya nuna cewa kwamandan rundunar sojin ruwan ƙasar, Shahram Irani, yana cewa dakarunsu sun sake karɓe jiragen ne lokacin da ma’aikatan Amurka da ke cikinsu suke barci.

Kara karanta wannan
Ina N450bn ta shiga? Atiku ya ɗauko magana mai girma kan tallafin manoma a Najeriya

Source: Getty Images
Sai dai rundunar sojin Amurka ta fito ta ƙaryata zargin a wani sako a X, tana mai cewa ikirarin da kwamandan Iran ya yi ƙarya ce da aka ƙirƙira.
Yadda Iran ta ce ta kwato jiragen
Rahoton Anadolu ya nuna cewa kwamandan sojin ruwan Iran, Shahram Irani, ya ce sojojin Amurka sun kwace jiragen dakon man fetur guda biyu na Iran.
Ya bayyana cewa dakarun Iran sun shiga jiragen lokacin da ma’aikatan da ke cikinsu suke barci, sannan suka yi nasarar kwato su.
Haka kuma, rahoton ya ambato Iran tana zargin sojojin Amurka da karɓar kuɗi daga masu jiragen ruwa domin ba su kariya yayin wucewa ta mashigar ruwan Hormuz.
Iran ta yi zargin cewa idan aka kai wa jiragen hari, sojojin Amurka ba sa amincewa da lamarin, kuma ba sa mayar da kuɗin da suka karɓa.
Amurka ta ƙaryata ikirarin Iran
Rundunar sojin Amurka ta mayar da martani kan ikirarin, inda ta bayyana cewa kwamandan sojin Iran ya yi zarge-zarge da dama marasa tushe cikin sa'o'i 24.
Ta ƙaryata cewa Iran ta kwato jiragen mai guda biyu, tana mai cewa babu rundunar sojin ruwa ta Iran da za ta iya gudanar da aikin da kwamandan ya bayyana.
Rundunar ta kuma musanta ikirarin cewa sojojin ruwan Iran sun kai hari kan jirgin ruwan yaƙin Amurka mai suna USS Abraham Lincoln a ranar farko ta Operation Epic Fury.
A cewar Amurka, jirgin bai fuskanci wani hari daga Iran ba, kuma rundunar jiragen yaƙin da ke tare da shi ta kammala aikinta a Gabas ta Tsakiya cikin nasara kafin ta koma Amurka a watan da ya gabata.
Haka kuma, Amurka ta musanta zargin cewa rundunar CENTCOM na karɓar dala miliyan 2.5 daga jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigar Hormuz.

Source: Getty Images
Ta ce babu kuɗin haraji da ake karɓa daga jiragen ruwa masu wucewa ta mashigar, tana mai cewa sojojinta da ƙawayenta na taimakawa wajen tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci.
Bayan baya
A wani labarin, kun ji cewa tattalin arzikin Faransa ya shiga koma baya bayan sababbin alkaluma sun nuna cewa ci gaban tattalin arzikin ƙasar ya ragu fiye da hasashen da aka yi a baya.
Hukumar S&P ta sauya hasashen darajar bashin ƙasar daga matsakaici zuwa mara kyau, sakamakon ƙaruwar matsin tattalin arziki da tsadar biyan ruwa kan basussuka.
Gwamnatin Faransa na fuskantar ƙalubalen rage gibin kasafin kuɗi zuwa kashi 5 cikin 100 na tattalin arzikin ƙasar a shekarar 2027, yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke matsowa.
Asali: Legit.ng

