Muhimman Abubuwa game da Zaben Gwaji da INEC ke Yi a Yau a Najeriya

Muhimman Abubuwa game da Zaben Gwaji da INEC ke Yi a Yau a Najeriya

  • Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta shirya gudanar da gwajin amfani da na’urorin tantance masu zaɓe da tura sakamakon zaɓe a ranar 28 ga Nuwamba, 2026
  • Za a gudanar da gwajin a rumfunan zaɓe 17,676 a faɗin Najeriya domin tantance ingancin na’urar BVAS da tsarin aika sakamakon zaɓe ta intanet
  • Hukumar ta buƙaci masu katin zaɓe da ke rumfunan da aka zaɓa su halarci gwajin domin taimaka mata gano matsalolin da ka iya tasowa kafin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Yayin da ake shirye-shiryen babban zaɓen 2027, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, 2026, domin gudanar da gwajin tantance masu zaɓe da aika sakamako.

Za a gudanar da gwajin a rumfunan zaɓe 17,676 a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja, domin tantance yadda na’urorin hukumar ke aiki da kuma gano matsalolin da ka iya kawo cikas a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan APC suka ci dalolin Atiku amma suka zaɓi Buhari a 2015

Zaben Gombe
Masu kada kuri'a a Gombe. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

A ina za a gudanar da gwajin?

A sakon da ta wallafa a X, INEC ta tsara gudanar da gwajin ne a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana.

Rahotanni sun nuna cewa a a gudanar da shi a rumfunan zaɓe biyu a kowace mazaba daga cikin mazabu 8,838 da ke faɗin ƙasar. Hakan ya sa jimillar rumfunan zaɓen da za a yi amfani da su ta kai 17,676.

Jihar Kano ce ke da mafi yawan rumfunan zaɓen da aka zaɓa, guda 968, sai Katsina mai 718 da Oyo mai 702.

A gefe guda, Abuja ce ke da mafi ƙarancin adadi, mai rumfunan zaɓe 124, sai Bayelsa mai 210 da Gombe mai 228.

A tsarin shiyyoyin siyasa, Arewa maso Yamma ce ke da mafi yawan rumfunan zaɓen, guda 4,002, wato kashi 22.7 cikin 100 na jimillar wuraren.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya fadi abin da zai hana Arewa karbar mulkin Najeriya a 2027

Arewa ta Tsakiya na da 2,785, Arewa maso Gabas kuma 2,418. Jimillar rumfunan da aka zaɓa a shiyyoyin Arewa uku ta kai 9,205, wato kashi 52.1 cikin 100.

Me ya sa za a yi gwajin?

Babban dalilin gudanar da gwajin shi ne tantance shirye-shiryen hukumar gabanin babban zaɓen 2027, tare da gano matsalolin fasaha da na gudanarwa tun kafin lokacin zaɓe.

Hukumar na son tabbatar da cewa na’urar BVAS tana aiki yadda ya kamata, tsarin tantance masu zaɓe yana tafiya ba tare da matsala ba, sannan ana iya aika sakamakon zaɓe ta intanet cikin nasara.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya taɓa sanar da shirin gudanar da gwajin yayin wani taro a cibiyar Chatham House da ke Landan.

Ya ce gwajin zai kwaikwayi zaɓen shugaban ƙasa domin hukumar ta tabbatar da ingancin na’urorin tantance masu zaɓe da tsarin aika sakamako kafin 2027.

Joash Amupitan
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Me INEC za ta gwada a lokacin?

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da hukumar za ta gwada shi ne na’urar BVAS, wadda ake amfani da ita wajen tantance masu zaɓe a rumfunan zaɓe.

Na’urar na amfani da hoton yatsun hannu da fuskar mutum wajen tabbatar da cewa mai zaɓe yana cikin waɗanda suka yi rajista kuma yana da damar kaɗa ƙuri’a.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban kasa ya daga zabe da shekara 2

A lokacin gwajin, INEC za ta duba yadda na’urorin ke aiki da kuma ko suna iya tantance masu zaɓe cikin sauri da inganci kamar yadda ake buƙata.

Haka kuma za a gwada tsarin aika sakamakon zaɓen gwaji ta intanet, ciki har da amfani da shafin IReV wajen bibiyar sakamakon.

Shin talakawa za su shiga gwajin?

INEC ta buƙaci masu katin zaɓe da ke rumfunan da aka zaɓa su shiga cikin gwajin, ba jami’an zaɓe kaɗai za su gudanar da shi ba.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa hukumar ta kuma ce masu zaɓen za su iya bibiyar sakamakon zaɓen kwaikwayo ta shafin IReV.

Saboda haka, mutanen da ke zaune a yankunan da aka zaɓa suna da rawar da za su taka wajen taimaka wa hukumar tantance tsarin.

Sai dai sanarwar da hukumar ta fitar ba ta yi cikakken bayani kan ko za a buƙaci masu zaɓe su gabatar da katin PVC, ko za a yi amfani da takardun ƙuri’a na gwaji, ko kuma yawan mutanen da ake sa ran za su shiga daga kowace rumfa ba.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa 5 da za su faru a 2027 su dauki hankalin duniya

Don haka, yana da kyau masu zaɓe su duba jerin rumfunan da aka zaɓa domin sanin ko tasu tana cikin waɗanda za a yi amfani da su.

Bayan kammala gwajin, zai dace INEC ta fitar da cikakken rahoto kan sakamakon da aka samu, matsalolin da aka gano da kuma matakan da za ta ɗauka domin gyara su kafin babban zaɓen 2027.

Kiran Uba Sani ga 'yan Arewa

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya buƙaci shugabannin siyasar Arewa su daina matsa lamba kan neman shugabancin ƙasa a zaɓen 2027.

Uba Sani ya ce Arewa na buƙatar ingantaccen tsarin ci gaba da zai nuna shirinta na jagorantar Najeriya, maimakon neman mulki bisa dalilin kasancewa daga yankin.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taro a Kaduna da aka shirya domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng