Jerin Fitattun Ƴan Kwallo 5 da Ake Hasashen Za Su Iya Lashe Kyautar Ballon d'Or 2025

Jerin Fitattun Ƴan Kwallo 5 da Ake Hasashen Za Su Iya Lashe Kyautar Ballon d'Or 2025

  • Ƙungiyar kwallon kafa ta PSG ta samu nasarar lashe gasar zakarun nahiyar turai, lamarin da ya jawo sabuwar muhawara kan kyautar Ballon d'Or ta 2025
  • Bayan kakar wasa mai ban mamaki da ya yi, tauraron PSG, Ousmane Dembele ya shiga gaba a manyan ‘yan wasan da ake ganin za su lashe wannan kambu
  • Ɗan wasan Barcelona Lamine Yamal, wanda ake kallonsa a matsayin magajin Lionel Messi, shi ma yana cikin waɗanda ake ganin za su iya lashe Ballon d'Or.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƙungiyar kwallon ƙafa ta kasar Faransa, Paris Saint-Germain watau PSG ta lashe kofin zakarun nahiyar turai 'UEFA Champions League' na farko a tarihinta.

PSG ta samu nasarar ɗaga kofin ne a ranar 31 ga Mayu, 2025, bayan ta doke ƙungiyar Inter Milan a wasan karshe da suka fafata a Munich.

Manyan zakakuran yan wasa 3 a nahiyar Turai.
Jerin yan wasan da ake ganin za su lashe kyautar Ballon d'Or Hoto: @dembouz, @lamineyamal, @MoSalah
Asali: Twitter

Kungiyar PSG ta samu wannan nasara karkashin jagorancin kocinta, Luis Enrique, wanda aka yaba da dabarunsa, kamar yadda ESPN ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kammala wannan wasa, hankalin duniya musamman masu bibiyar ƙwallon ƙafa ya koma kan kyautar gwarzon ɗan kwallo na duniya wacce aka fi sani da Ballon d'Or.

Ana sa ran za a sanar da wanda ya lashe Ballon d'Or a watan Oktoba, 2025 a birnin Farisa na ƙasar Faransa.

Legit.ng ta duba wasu daga cikin fitattun ‘yan wasan da ake ganin sune kan gaba wajen lashe wannan gagarumar kyauta a bikin da za a gudanar a birnin Paris.

1. Ousmane Dembele (PSP/Faransa)

A halin yanzu, ɗan wasan PSG ɗan asalin ƙasar Faransa, Ousmane Dembele, shi ne kan gaba a jerin waɗanda ka iya kambun Ballon d’Or na bana.

Idan har ɗan wasan ya samu nasara, kyautar za ta dawo hannun ɗan ƙasar Faransa karon farko tun bayan nasarar Karim Benzema a 2022.

Dan wasan PSG, Ousmane Dembele.
Dan wasan PSG da Faransa, Demeble shi ne a kan gaba a jerin wadanda ka iya lashe Ballon d'Or Hoto: @dembouz
Asali: Facebook

Ko da yake bai jefa kwallo ba a wasan karshe na Champions League, ya taimaka wajen zura kwallaye biyu, wanda hakan ya ɗaga jimillar nasarorinsa na kakar bana zuwa kwallaye 33 da taimako 15, a cewar Foot Boom.

Yayin da ake sa ran sanar da wadanda za a bai wa kyautar a watanni masu zuwa, ana jiran a gani ko Dembele zai maye gurbin Rodri, wanda ya lashe kyautar a 2024.

2. Lamine Yamal (Barcelona/Sifaniya)

A shekaru 17 kacal da haihuwarsa, ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal ya tabbatar da kansa a matsayin magajin fitaccen ɗan wasan nan, Lionel Messi a kulob ɗin.

Matashin ɗan wasan ya taka rawar gani wajen taimaka wa kulob ɗin lashe kofunan gida uku, inda ya zura kwallaye 18 tare da bayar da taimako 25.

Sai dai, duk da yana fatan lashe gasar ƙasashen turai, watau UEFA Nations League tare da tawagar ƙasar Sifaniya, rashin nasara a gasar Champion ta 2025 na iya hana shi lashe kyautar Ballon d’Or.

Matashin dan wasan Barca, Lamine Yamal.
Lamine Yamal na cikin jerin wadanda za su iya lashe kyautar gwarzon dan wasa watau Ballon d'Or Hoto: @Barcauniversal
Asali: Twitter

3. Raphinha (Barcelona/Brazil)

Abokin wasan Lamine Yamal, Raphinha, ya nuna bajinta matuƙa a kakar wasan da aka kammala 2024/2025.

A cewar jaridar GOAL, Raphinha na ɗaya daga cikin ‘yan wasa da suka taso suka nuna hazaƙa a Turai a ƙarƙashin horon sabon koci, Hansi Flick.

Dan wasan Barcelona, Raphinha ya fi kowa zura kwallaye a raga
Raphinha shi ne a kan gaba wajen zura kwallaye da taimakawa a bana Hoto: @Raphinha
Asali: Twitter

Tsohon tauraron ƙungiyar Leeds United shi ne kan gaba wajen zuwa ƙwallaye da taimakawa a manyan lig-lig biyar na nahiyar Turai.

Raphinha ya zura ƙwallaye 34 a raga, sannan ya taimaka an jefa wasu 25, lamarin da ya taimaka matuƙa wajen nasarorin da ƙungiyar Barcelona ta samu.

Tabbas Raphinha na cikin masu ƙwazo da kuma manyan ƴan wasa na sahun gaba da ka iya don lashe Ballon d’Or.

4. Mohamed Salah (Liverpool/Masar)

Ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah yana cikin fitattun ‘yan wasan kwallon ƙafa da ake hasashen za su lashe lambar yabon Ballon d’Or tun farkon kakar 2024/2025.

Mo Salah ya zura kwallaye 34 a raga tare da taimakawa wajen zura wasu ƙwallaye 23 a kaka guda, cewar rahoton Football Transfers.

Hakan ya taimaka wa Liverpool ta samu damar lashe kofin Firimiya na ƙasar Ingila a ƙarƙashin sabon koci Arne Slot.

Dan wasan Liverpool ya taka rawar gani a Firimiya
Mohammed Salah shi ne ya lashe kambun gwarzon ɗan wasan Firimiya 2024/2025 Hoto: @Touchlinex
Asali: Twitter

Sai dai, ficewar Liverpool daga gasar zakarun turai a zagaye na 16 hannun PSG na iya rage masa dama, duk da cewa ya nuna bajinta matuƙa a kakar wasan 2024/2025 a Anfield.

5. Kylian Mbappe (Real Madrid/Faransa)

Dan wasan na Faransa da Real Madrid, Mbappe shi ne ya zo na shida a bikin Ballon d’Or na bara, kuma duka waɗanda ke gabansa a wancan lokacin babu su a bana.

Mbappé ya lashe kofunan Uefa Super Cup da Intercontinental Cup, amma ya rasa La Liga a hannun Barcelona sannan kuma Arsenal ta fitar da Real Madrid daga gasar Zakarun Turai.

Rahoton Goal ya nuna cewa ɗan wasan ya zura ƙwallaye 43 tare da taimaka wa wajen jefa biyar a kakar wasan da aka ƙaraƙare kwanan nan.

Dan wasan gaba a Real Madrid, Kylian Mbappe.
Mabappe shi ne wanda ya lashe kyautar ɗan kwallon da ya fi zura kwallaye a Laliga Hoto: @KMbappe
Asali: Twitter

Ronaldo ya ce ba a taɓa kamarsa a kwallon kafa

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen ɗan wasa ɗan asalin ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya ce shi ne ya fi kowa iya taka leda a tarihin wasan kwallon kafa a duniya.

Ronaldo, wanda ya kai kimanin shekaru 40 a duniya, ya bugi ƙirjin cewa babu wani ɗan wasan kwallo ya taɓa kai matsayin da ya kai a kwallon kafa.

Ɗan wasan ya ce saura ƙiris ya cimma yarjejenuyar komawa ƙungiyar kwallon ƙafa da Barcelona kafin ya tafi Manchester United.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262