UCL: Kungiyoyin Kwallon Kafa 5 da Suka Fi Lashe Gasar Zakarun Turai a Tarihi
Gasar zakatun Turai da aka fi sani da Champions Leagus shi ne gasa mafi girma da daraja da ake bugawa a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a Nahiyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Madrid, Spain - Lashe gasar Champions League ya kasance abu mafi muhimmanci a wurin kungiyoyin kwallon kafa da dama a Nahiyar Turai.
Samun nasara a gasar ya kasance burin kowace kungiya da ke buga kwallo musamman a manyan gasa kamar Firimiya, La Liga, Serie A, Bundesliga da Ligue 1.

Source: Getty Images
Kungiyoyin da suka fi lashe Champions League
Lashe gasar sau biyar ko fiye da haka na sanya kungiya cikin jerin manyan sarakunan kwallon kafa na duniya, cewar OneFootball.
A tarihin gasar, kungiyoyi biyar kacal ne suka kai wannan matsayi mai girma, Legit Hausa ta duba kungiyoyin da tarihin samun nasara a gasar.
1. Real Madrid — Kofuna 15
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ita ce sarauniya a gasar bayan yin fice a cikin sauran kungiyoyi da ke buga gasar.
Real Madrid ita ce kungiya ta farko da ta fara lashe gasar a shekarar 1956 wanda kuma ta kasance wacce tafi kowa yin nasara a gasar har sau 15.
Shekarun da Real Madrid ta lashe gasar sun hasa da 1956, 1957, 1958, 1959, 1960, 1966, 1998, 2000, 2002, 2014, 2016, 2017, 2018, 2022, 2024.
Ita ce kadai kungiyar da ta lashe gasar Champions League daga baya sau uku a jere tsakanin 2016 zuwa 2018.
Kungiyar ta samar da fitattun taurari kamar Alfredo Di Stefano, Cristiano Ronaldo, Zinedine Zidane, Luka Modric, Kylian Mbappe da Vinicius Junior da sauransu a jiya da yau.

Source: Getty Images
2. AC Milan — Kofuna 7
Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan da ke buga gasar Serie A a Italiya ta zama kungiyar ta biyu mafi daraja a gasar.
AC Milan ta yi kokarin lashe gasar har sau 7 wanda ya sanya ta cikin jerin kungiyoyi masu daraja duk da yanzu ta dade rabonta da lashe gasar.
Shekarun da ta lashe gasar sun hada da 1963, 1969, 1989, 1990, 1994, 2003, da kuma shekarar 2007.
AC Milan ita ce kungiyar Italiya mafi nasara a gasar Nahiyar Turai, ta mamaye kwallon Turai a karshen shekarun 1980 da farkon shekarun 1990.

Source: Getty Images
3. Liverpool FC — Kofuna 6
Liverpool da ke buga gasar Firimiya a kasar Birtaniya tana daga cikin manyan kungiyoyi inda suka taka rawar gani a gasar zakarun Turai.
Kungiyar ta zama ta uku daga cikin kungiyoyi masu daraja wacce ta lashe gasar Champions League har sau shida a duniya.
Shekarun da ta lashe gasar zakarun Turai sun hada da shekarar 1977, 1978, 1981, 1984, 2005 da kuma 2019, kamar yadda shafin UEFA.com ya wallafa.
Liverpool ita ce kungiyar Birtaniya mafi nasara a tarihin gasar Champions League, an san kungiyar da magoya bayanta masu zafi da taken ta na "You'll Never Walk Alone".

Kara karanta wannan
Amurka ta tabbatar da kulla hadin gwiwa, za ta kara kawo hare hare cikin Najeriya

Source: Getty Images
4. Bayern Munich — Kofuna 6
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta na buga gasar Bundesliga a Jamus inda ta kasance mafi girma a kasar idan ana maganar lashe kofuna.
Bayern Munich ta yi kokarin lashe gasar a shekarun 1974, 1975, 1976, 2001, 2013 da kuma shekarar 2020, cewar Sky Sport.
Kungiyar ita ce kungiyar Jamus mafi nasara a gasar Turai, ta lashe kofunan Turai uku a jere a shekarun 1970.
Bayern ta gina tarihinta ne kan taurari kamar Franz Beckenbauer, Gerd Muller da irinsu Thomas Muller da Robert Lewandowski a shekarun nan.

Source: Getty Images
5. FC Barcelona — Kofuna 5
Barcelona wacce ta lashe gasar La Liga har shekaru biyu a jere a kakar wasa ta 2024/2025 da kuma 2025/2026, ta kasance na biyu mafi daraja a gasar Champions League a Spain.
Kungiyar kwallon kafar ta yi nasarar lashe gasar Champions Leagus a shekarun 1992, 2006, 2009, 2011 da kuma 2015, cewar shafin kungiyar Barcelona.
Barcelona ta shahara da salon wasan mallake kwallo da ake kira "tiki-taka", kungiyar ta kai kololuwar nasara karkashin jagorancin koci Pep Guardiola.
Ta samar da wasu daga cikin manyan 'yan wasan kwallon kafa a tarihi kamar Lionel Messi, Ronaldinho, Suarez, Xavi, Iniesta, sannan yanzu akwai Raphinha, Lamine Yamal da sauransu.
Kungiyar Barcelona ta shekarar 2009 ta zama kungiyar Spain ta farko da ta lashe 'Copa Del Rey, kofin La liga da kuma Champions League a kakar wasa guda.

Source: Getty Images
Bayan shekaru 22, Arsenal ta lashe gasar Firimiya
A baya, an ji cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta Birtaniya ta kafa tarihi a gasar firimiya ta bana da ake bugawa ta shekarar 2025/2026.
Arsenal ta yi kokari sosai, ta samu ta lashe kofin gasar Firimiya ta kasar karo na farko cikin shekara 22 da suka gabata.
Hakan na zuwa ne bayan Manchester City ta yi kunnen doki da Bournemouth ranar Talata 19 ga watan Mayun 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


