Tawagar Iran za Ta Shiga Amurka, Ministan Trump Ya Ce Babu Matsala
- An bai wa tawagar ƙwallon ƙafar Iran bizar shiga Amurka gabanin gasar kofin duniya da za a fara mako mai zuwa, kamar yadda jami’an kasar suka fada
- An amince da bayar da bizar ne kwanaki 10 kacal kafin wasan farko na tawagar da New Zealand, wanda za a buga a Los Angeles ranar 15 ga Yunin 2026
- Amurka ta bayar da bizar da ake buƙata domin Iran ta shiga gasar kofin duniya, ciki har da ta ‘yan wasa da wasu ma’aikatan da za su tallafa masu a gasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - ‘Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar Iran da za su halarci gasar kofin duniya sun samu bizar da za ta ba su damar shiga da kuma fafatawa a Amurka.
Tun a kwanakin baya aka yi ta takaddama kan ko 'yan wasan kasar za su taka leda a Amurka lura da yakin da ya barke da Iran a Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
'Yan wasan Iran za su je Amurka
ABC ta wallafa cewa Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya nuna cewa gwamnatin Trump ba ta da wata matsala wajen bayar da bizar ga tawagar Iran yayin da yake magana a majalisar dokoki a farkon wannan makon.
Sai dai Rubio ya ce Amurka ba za ta bari gwamnatin Iran ta yi amfani da taron wajen shigar da mutanen da ke da alaƙa da IRGC ba.
“Abin da ba za mu bari ba shi ne su haɗa wasu mutane da muka san ba su da wata alaƙa da wasanni kuma suna da alaƙa da IRGC ko makamancin haka a cikin tawagarsu, don haka za mu sanya ido sosai kan hakan,”
In ji shi.
Bayanin Jakadan Amurka
Jakadan Amurka a Turkiyya, Tom Barrack, ya wallafa sako a shafin X ranar Juma’a yana cewa ya yi farin ciki da matakin da kasar shi ta dauka.
“Ina alfahari da ƙwararrun ma’aikatanmu a ofishin jakadancin Amurka da ke Ankara saboda aikinsu wajen bayar da biza ga tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar Iran a hanyarsu ta zuwa gasar kofin duniya a Amurka.”
“Kuma muna sa ran maraba da ‘yan wasa da magoya baya daga ko’ina cikin duniya,”
In ji shi, yayin da ya sake wallafa wani rahoto daga Al Jazeera da ke cewa an bai wa tawagar Iran biza domin 'yan wasan su shiga Amurka.

Source: Getty Images
Tawagar Iran za ta buga wasanninta a Amurka amma ana sa ran za ta zauna a Mexico saboda wasu matsaloli da suka shafi takunkuman da Amurka ta kakaba.
Iran ta yi watsi da bukatar Trump
A wani labarin, kun ji cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi watsi da batun neman Ayatollah Mojtaba Khamenei ya gana da Donald Trump.
A makon da ya wuce Trump ya shaida cewa zai so gana wa da Mojtaba Khamenei a lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar hakan.
An naɗa Ayatollah Mojtaba Khamenei a matsayin jagoran Iran a watan Maris, 2026 bayan mutuwar mahaifinsa kuma wanda ya gabace shi, Ali Khamenei.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

