Kano Pillars: Kyaftin Ahmed Musa Ya Samu Babban Mukami a Gwamnatin Abba Gida Gida

Kano Pillars: Kyaftin Ahmed Musa Ya Samu Babban Mukami a Gwamnatin Abba Gida Gida

  • Gwamna Abba Yusuf ya naɗa Ahmed Musa matsayin Manajan Kano Pillars, tare da kafa sabon kwamitin gudanarwa don inganta ƙungiyar
  • An sake naɗa yawancin mambobin kwamitin da ya gabata, domin ƙarfafa ƙungiyar kafin a fara kakar Firimiyar Najeriya (NPL) mai zuwa
  • Gwamnatin Abba na sa ran nadin Ahmed Musa zai kawo ci gaba a taka ledar 'yan wasa da kuma jawo hankalin duniya ga Kano Pillars

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin tsohon kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa a matsayin Janar Manaja na kungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars.

Legit Hausa ta fahimci cewa, nadin Ahmed Musa na zuwa ne a lokacin da Gwamna Abba Yusuf ya kafa sabon kwamitin gudanarwa na ƙungiyar Kano Pillars.

Gwamna Abba Yusuf ya nada Ahmed Musa matsayin manajan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars
Kyaftin Ahmed Musa tare da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. Hoto: Ahmed Musa MON
Asali: Facebook

Abba ya nada sababbin shugabannin Kano Pillars

Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnan Kano ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa kafa sabon kwamitin ya zo ne bayan karewar wa'adin tsohon kwamitin na shekara guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na daga cikin ƙoƙarin da gwamnati ke yi domin ƙarfafa kulob din da kuma inganta aikinta kafin a shiga sabuwar kakar gasar Firimiyar Najeriya, NPFL.

Sanarwar Dawakin Tofa ta ce:

"Sabon naɗin ya biyo bayan cikar wa’adin shekara guda da aka bai wa tsohon kwamitin, wanda ya jagoranci Kano Pillars zuwa matsayi na 9 a teburin NPFL.
"Sakamakon yadda kwamitin ya yi aiki a baya, an sake naɗa yawancin mambobinsa a sabon kwamitin, tare da ƙara sababbin mutane a ciki domin ci gaban kungiyar."

Sababbin shugabannin gudanarwar Kano Pillars

Ga jerin sababbin shugabanni da mambobin kungiyar kwallon kafar Kano Pillars:

  1. Ali Muhammad Umar (Nayara) – Shugaba
  2. Salisu Mohammed Kosawa – Mamba
  3. Yusuf Danladi Andy Cole – Mamba
  4. Idris Malikawa Garu – Mamba
  5. Nasiru Bello – Mamba
  6. Muhammad Ibrahim (Hassan West) – Mamba
  7. Abdulkarim Audi Chara – Mamba
  8. Muhammad Danjuma Gwarzo – Mamba
  9. Mustapha Usman Darma – Mamba
  10. Umar Dankura – Mamba
  11. Ahmad Musbahu – Mamba
  12. Gambo Salisu Shuaibu Kura – Mamba
  13. Rabiu Abdullahi – Mamba
  14. Aminu Ma’alesh – Mamba
  15. Safiyanu Abdu – Mamba
  16. Abubakar Isah Dandago Yamalash – Daraktan yaɗa labarai I
  17. Ismail Abba Tangalash – Daraktan yaɗa labarai II

Gwamnatin Kano na fatan Ahmed Musa zai kai Kano Pillars ga nasara a NPL da jawo masu zuba jari
Fitacccen dan wasan kwallon kafa kuma tsohon kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa. Hoto: Ahmed Musa MON
Asali: Getty Images

Abba ya nada Ahmed Musa Manajan Kano Pillar

A wani muhimmin mataki, Gwamna Abba ya amince da naɗin Ahmed Musa, fitaccen ɗan kwallon kafa na duniya kuma tsohon tauraron Kano Pillars, a matsayin babban manajan Kano Pillars.

Ana sa ran nadin Ahmed Musa, wanda ya shahara a matakin ƙasa da na ƙetare a manyan gasar ƙwallon kafa da Super Eagles, zai kawo ƙwarewar shugabanci da kuma jawo hankalin duniya ga kulob din.

“Naɗin Ahmed Musa ya nuna burinmu na haɗa ƙwarewar aiki da ƙwarewar buga ƙwallon kafa. Muna da yakinin kasancewarsa a kulob din zai karfafa 'yan wasa, jawo masu zuba jari, da kuma farfaɗo da sha’awar masu kallo kan kulob din," inji sanarwar.

Ana sa ran Kano Pillars FC, wacce ta kasance ɗaya daga cikin manyan kulob-kulob din ƙasar nan, za ta ga gagarumin sauyi a taka leda da ci gaban kungiyar karkashin Ahmed Musa da tawagarsa.

Abba Yusuf ya nada Ahmed Musa Ambasada

Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kano ta ba KyaftinAhmed Musa, muƙamin jakadan wasanni na jihar bisa gudunmawarsa ga ci gaban kwallon ƙafa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da naɗin, a wani mataki na karfafa harkokin wasanni da haɗin gwiwa da fitattun ƴan wasa na jihar.

Ahmed Musa, ɗan wasan Kano Pillars a baya, ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa wannan karamci da girmamawa da aka yi masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.