Sunaye: Gwamnan Kano, Abba Ya Nada Mutum 19 Masu Taimaka Masa na Musamman
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin ƙarin manyan mataimaka na musamman (SSA) 19 don ƙarfafa shugabanci a Kano
- Daga cikin wadanda aka nada akwai Sunusi Kata Madobi, matsayin SSA na Rediyo I, wanda zai maye gurbin marigayi Abdullahi Tanka
- Gwamna Abba Yusuf na fatan sababbin hadiman za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen ba da gudunmawa ga ci gaban jihar Kano
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano – Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin ƙarin manyan mataimaka na musamman (SSA) guda 19.
Wannan nadin na daga cikin matakan da Gwamna Abba Yusuf yake dauka domin ƙara ƙarfafa shugabanci da inganta isar da ayyukan ga al’ummar jihar.

Asali: Facebook
Gwamna Abba ya nada manyan hadimai 19
An tabbatar da wannan nadin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Naɗin waɗannan mataimaka na musamman na nuni da ci gaba da ƙoƙarin gwamnatin Kwankwasiyya a Kano na tabbatar da ingantaccen mulki da ya dace da buƙatun al’umma.
Sanarwar Sanusi Bature Dawakin Tofa ta ce:
"Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin ƙarin manyan masu taimaka masa na musamman (SSA) domin ƙarfafa shugabanci da inganta isar da ayyuka a jihar."
Sunayen sababbin hadiman gwamnan Kano
An raba muƙaman ga sababbin hadiman kamar haka:
S/N | Sunaye | Mukami | Wurin Aiki |
1 | Hon. Sunusi Kata Madobi | Babban mataimaki na musamman (SSA) | Rediyo I |
2 | Mika’ilu Shu’aibu (Ghari) | SSA | Hisbah |
3 | Muhktar Abdullahi Shuwaki (Ghari) | SSA | Filaye |
4 | Engr. Sagir Lawan Waziri (Ghari) | SSA | Harkokin al'umma da tallafi |
5 | Najeef Abdulsalam | SSA | Yan Akwati (Maza) |
6 | Huwaila Iguda | SSA | Yan Akwati II (Mata) |
7 | Naziru Hamidu Bako | SSA | KAROTA |
8 | Usman Abbas Sunusi | SSA | Mai kula da tsare-tsare na II |
9 | Engr. Usman Kofar Naisa | SSA | Filin wasanni na Mahaha |
10 | Danladi Alhassan Mai-Bulala | SSA | Tattaro kan jama'a na II |
11 | Abdulkhadir Umar Kwankwaso | SSA | Ilimi (Abuja) |
12 | Balarabe Aminu Yusuf | SSA | Harkokin gida na III (Gidan bakin gwamnati) |
13 | Shukurana Garba Langel | SSA | Tattaro kan jama'a - Kano ta Arewa |
14 | Mustapha Ma'aruf Diso | SSA | Kiwon lafiya a matakin farko |
15 | Garba Yahaya Labour | SSA | Zirga-zirga (I) |
16 | Humaira Sharif | SSA | Wayar da kan mata |
17 | Muttaka Sani Gaya | SSA | Kungiyoyin magoya baya na III |
18 | Gausu Nuhu Wali | SSA | Fasahohin gargajiya |
19 | Hadiza Sale (Baby) | SSA | Tsaftar muhalli |

Asali: Twitter
Fatan gwamnati ga sababbin hadimai 19
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kyakkyawan fata cewa sababbin hadiman za su yi amfani da gwanintarsu da kuma kwazonsu wajen ba da gudunmawa ga ci gaban jihar.
Ta bakin Sanusi Dawakin Tofa, Gwamna Abba Yusuf ya ce yana fatan wadanda ya nada za su taimaka masa wajen samawa al'ummar Kano ayyukan more rayuwa.
An sa ran wannan ƙarin hadiman zai ƙara inganta ayyukan gwamnati a sassa daban-daban, tare da bai wa gwamnatin damar isar da ayyukanta ga birane da kauyuka.
Abba ya nada Ahmed Musa manajan Kano Pillars
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Yusuf ya naɗa Ahmed Musa a matsayin sabon manajan Kano Pillars, tare da kafa sabon kwamitin gudanarwa don farfaɗo da ƙungiyar.
An sake nada yawancin tsofaffin mambobin kwamitin da ya jagoranci ƙungiyar a kakar da ta gabata an sake, tare da ƙarin sababbin fuska domin tunkarar kakar Firimiyar Najeriya (NPL).
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa nadin Ahmed Musa, wanda fitaccen ɗan wasa ne a duniya, zai kawo sabon salo, ƙwarewa da ɗaukaka ga ƙungiyar Kano Pillars a matakin ƙasa da ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng