Abubuwa 5 da Suka Taimaka wa Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya bayan Shekaru 22
London - Kungiyar Arsenal ta kawo ƙarshen dogon jiran shekaru 22 bayan da ta zama zakarar gasar firimiya a ranar Talata, bayan Manchester City ta tashi 1-1 da Bournemouth.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ƙungiyar Mikel Arteta ta shawo kan ƙalubalen da Pep Guardiola da Manchester City suka kawo, inda ta tabbatar da nasarar lashe gasar ana saura wasa ɗaya a kammala kakar bana.

Source: Getty Images
Wannan nasara ta zo ne bayan Arsenal ta shafe shekaru uku tana karewa a matsayi na biyu, lamarin da ya jefa magoya bayan ƙungiyar cikin takaici, kamar yadda rahoton Sky Sport ya nuna.
Ga wasu manyan dalilai 5 da suka taimaka wa Arsenal ta lashe kofin firimiyar bana bayan shekaru 22 tana jira:
1. David Raya ya zama ginshikin nasara
Mai tsaron ragar Arsenal, David Raya, ya lashe kyautar gwarzon mai tsaron raga karo na uku a jere saboda yawan kammala wasa ba tare da an zura masa kwallo da ya yi a gasar firimiya.
Sai dai kakar bana ta kasance mafi kyau a gare shi tun bayan komawarsa Arsenal daga Brentford a shekarar 2023.
Raya ya taka muhimmiyar rawa a wasu muhimman wasanni da Arsenal ta yi nasara da ci 1-0 a kan Manchester United da West Ham.
A wasan farko na kakar bana, David Raya ya hana Manchester United cin kwallo bayan ya kakkabe hare-hare da dama, cewar rahoton RFI.
Haka kuma, a wasan da Arsenal ta doke West Ham, an soke kwallon da West Ham ta ci a ƙarshen wasa bayan na'urar VAR ta tabbatar an yi wa Raya laifi.
2. Cin kwallaye bayan tsayawar wasa
Aljazeera ta ruwaito cewa fiye da kaso 40 cikin 100 na ƙwallayen Arsenal a gasar firimiya ta bana sun fito ne daga bugun kwallaye bayan an tsayar da wasa.
Daga cikin ƙwallaye 28 da ta ci ta irin wannan hanya, guda 18 sun fito ne daga bugun kusurwa, wanda ya kafa sabon tarihi a gasar firimiya.
Masu adawa da Arsenal suna yi mata lakabi da “Set Piece FC” saboda yadda take amfani da bugun 'bayan tsayawar wasa' wajen cin ƙwallaye.
Koci na musamman Nicolas Jover ya samar da dabaru masu inganci da suka bai wa Arsenal damar cin moriyar wannan tsari.
Ƴan wasa irin su Bukayo Saka da Declan Rice sun taimaka sosai wajen aika ƙwallaye masu kyau cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron gida.
3. Declan Rice ya taka rawa sosai

Source: Getty Images
Ko da yake Bruno Fernandes ne ya lashe kyautar gwarzo na marubutan wasanni, Declan Rice ya kasance ginshiƙi ga Arsenal.
Tun bayan da Arsenal ta kashe sama da fam miliyan 100 wajen sayensa shekaru uku da suka wuce, Rice ya nuna ƙwazo sosai.
Dan wasan tsakiyar ya taka fiye da minti 4,000 a gaba daya gasar bana ta firimiya, kamar yadda Independent ta ruwaito.
Ya zura kwallaye huɗu tare da bayar da taimakon cin ƙwallaye biyar a firimiyar bana.
Sai dai mafi girman gudunmawarsa ita ce ƙwazon da yake yi wajen taimaka wa tsaro, lamarin da ya sa Arsenal ta zama ƙungiyar da aka fi wahalar zura wa ƙwallo a bana.
4. Tulin ƴan wasa ya taimaka wa Arsenal
A kakar da ta gabata, raunin da ƴan wasa suka samu ya hana Arsenal lashe gasar. Sai dai a bana, Arteta ya ƙarfafa ƙungiyarsa da sababbin ƴan wasa masu inganci.
Duk da raunin da Bukayo Saka, Martin Odegaard, Mikel Merino, Kai Havertz da wasu suka samu, Arsenal ta ci gaba da nuna ƙarfi a wasanninta, a cewar rahoton Super Sport.
Sababbin ƴan wasa irin su Eberechi Eze, Martin Zubimendi, Viktor Gyokeres, Noni Madueke da Piero Hincapie sun taimaka wajen tabbatar da nasarar ƙungiyar.

Source: Getty Images
5. City da Liverpool sun gaza
Arsenal, wadda attajirin Afrika, Aliko Dangote ya so ya saya, ta taba samun maki fiye da haka shekaru biyu da suka gabata amma Manchester City ta ƙwace mata kofin.
A cikin shekaru goma da suka gabata, City da Liverpool sun saba lashe gasar da sama da maki 90. Sai dai a bana maki 82 suka isa Arsenal ta zama zakara.
Manchester City ta rasa daidaito da ƙwazon da ta saba nunawa a zamanin Pep Guardiola, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Haka kuma Liverpool ta kasa kare kambunta yayin da Manchester United ta kare a matsayi na uku duk da korar Ruben Amorim a tsakiyar kakar wasa.
Arsenal ta lashe gasar firimiyar bana
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Arsenal da kocinta, Mikel Arteta sun kafa tarihi a gasar firimiya da ake yi a kasar Birtaniya.
Kungiyar Arsenal ta zama zakarar gasar Firimiya ta Birtaniya ta kakar 2025/2026 wanda hakan ya biyo bayan shafe shekaru 22 ba tare da lashe gasar ba.
Za a karrama kungiyar ta Arewacin London a filin wasa na Selhurst Park bayan wasansu da Crystal Palace a ranar Lahadi mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



