Gwamnatin Kano Ta Dauki Mataki Kan Tawagar Kano Pillars Bayan Gaza Cin Wasanni

Gwamnatin Kano Ta Dauki Mataki Kan Tawagar Kano Pillars Bayan Gaza Cin Wasanni

  • Gwamnatin Kano ta nuna damuwa kan yadda tawagar 'Sai Masu Gida' ke shan kaye a wasannin da ta buga a 'yan kwanakin nan
  • Kwamishinan wasanni na Kano, Hamza Kachako ya ba tawagar wa'adin wasanni uku ta dawo da martabarta a gasar Firimiyar Najeriya
  • A baya-bayan nan Kano Pillars ta kwashi kashinta a hannun tawagar Benin (2-1), Shooting Stars (1-2) da Enyimba (5-0)

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf a jihar Kano ta ba kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars wa'adin wasanni uku domin ta dawo da martabarta a fagen daka leda.

Gwamnatin Abba ta ba Kano Pillars wa'adin wasanni uku ta dawo da martabarta
Kano Pillars ta kwashi kashinta a hannu a wasannin baya-bayan na da ta buga. Hoto: Kano Pillars
Asali: Facebook

Hamza Safiyanu Kachoka, kwamishinan riko na ma'aikatar matasa da wasanni ta jihar Kano ya sanar da ba da wa'adin kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta fara ƙera motoci gadan-gadan, gwamnatin tarayya ta yi bayani

Bayar da wa'adin na da nasaba da rashin tabuka abin kirki da tawagar Pillars ta yi a wasanninta na baya-bayan nan a gasar Firmiyar Najeriya 2023/2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Firimiyar Najeriya: An lallasa Kano Pillars

Kano Pillars da ake wa take da 'Sai Masu Gida' ta fuskanci rashin sa a a wasanta na karshe tsakaninta da Bendel Insurance ta Benin wanda aka tashi da ci 2-1.

Ko kafin wannan, Kano Pillars ta kwashi kashinta a hannun tawagar Shooting Stars (1-2) da Enyimba (5-0).

Kachako ya karfafi guiwar tawagar Kano Pillars tare da basu tabbacin goyon bayan gwamnatin Abba Kabir Yusuf na ganin sun yi nasara a wasannin su na gaba.

Wasannin Kano Pillars na gaba

Haka kuma ya tunatar da su muhimmancin wannan wa'adi da aka ɗebar masu na dawowa da matabar kungiyar, yana mai cewa gwamnati ba za ta kuma lamuntar rashin nasara ba.

Kara karanta wannan

A karon farko cikin kwanaki, naira ta ci karo da matsala, ta tashi da 1.3% a kasuwa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kano Pillars za su kara da Gombe United a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu a filin wasanni na Sani Abacha da ke Kano.

Bayan wannan wasan ne kuma tawagar 'Sai Masu Gida' za ta kara da Akwa United a wasan waje, da kuma wasan gida da tawagar Doma United ta jihar Gombe.

A halin yanzu dai Kano Pillars na a mataki na 7 a teburin Firmiyar Najeriya da maki 41 daga wasanni 30 da ta buga.

Kano Pillars ta durkusa gaban NFFL

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta durkusa gaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta roki afuwa kan tarar da aka kakaba mata.

Hukumar NFFL ta kakabawa Kano Pillars tarar Naira miliyan 12 sakamakon tayar da tarzoma a filin wasa na Kano a wasanta da Plateau United.

Asali: Legit.ng

Online view pixel