Matar Tsohon Sanata Ta Shiga Matsala, Minista Ya Bukaci Gudanar da Bincike Kanta

Matar Tsohon Sanata Ta Shiga Matsala, Minista Ya Bukaci Gudanar da Bincike Kanta

  • Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya umarci a gudanar da bincike kan matar tsohon sanata a Najeriya
  • Ana zargin matar tsohon sanata Elisa Abbo da shiga wuraren da aka haramta a filin jirgin saman Yola da ke Adamawa
  • Bidiyon da aka samu ya nuna matar tana raka mijinta har zuwa matattakalar jirgi, lamarin da ya jawo maganganu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - Ministan sufurin jiragen sama da bunkasa sararin samaniya, Festus Keyamo, ya buƙaci bincike kan matar tsohon sanata.

Keyamo ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan matakan tsaro a filin jirgin saman Yola bayan rahotanni sun bayyana karya dokokin tsaro.

Minista ya bukaci binciken matar tsohon minista
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo da Sanata Ishaku Abbo da matarsa. Hoto: Patience Ishaku Abbo, Festus Keyamo.
Source: Facebook

Premium Times ta ce matakin ya biyo bayan wallafa wasu bidiyoyi da suka nuna matar Sanata Ishaku Abbo tana saba ka'ida.

Kara karanta wannan

"Za a iya gano su"; Buratai ya dauko batun 'yan bindigan da ke fitowa a bidiyoyi

Yadda matar tsohon sanata ta saba ka'ida

An nuna matar tana shiga wuraren da aka kebe ga ma'aikata da fasinjoji kawai wanda hakan ya saba ka'ida a hukumar.

Rahotanni sun ce ministan ya bukaci jami'an tsaro su yi bayani kan yadda lamarin ya faru bayan rahoton farko ya bayyana, lamarin da ya jawo hankalin ma'aikatar.

Jami'an tsaron filin jirgin sun ce Patience Abbo ta sanar da su cewa tana tafiya tare da mijinta, saboda haka aka ba ta damar wucewa ta kofar shiga.

A cewar shugaban tsaro na filin jirgin, jami'an sun fahimci cewa ba fasinja ba ce kawai bayan sun ga ta dawo ita kadai daga yankin da jirgin yake.

Sai dai wani sabon bidiyo da aka samu daga baya ya nuna ta sake rakiyar mijinta zuwa kusa da matakalar jirgi tana tura wata akwati mai launuka daban-daban.

Minista ya nuna damuwa game da saba dokoki a filin jirgin sama
Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo. Hoto: @fkeyamo.
Source: Facebook

Abin da dokokin hukumar suka tanada

Masana harkar sufurin jiragen sama sun ce bayanin jami'an tsaron ya haifar da tambayoyi masu yawa kan bin dokokin tsaro na kasa da na duniya.

Kara karanta wannan

Minista a Isra'ila na zuga Netanyahu, yana neman a fara yi wa Amurka bore

Dokokin sufurin jiragen sama na Najeriya sun tanadi cewa yankunan da jirage ke aiki wurare ne masu matukar kariya, inda sai masu izini ko fasinjoji masu takardun tafiya kadai ake bari, cewar Leadership.

Masana sun tambayi dalilin da ya sa jami'an tsaro suka dogara da bayanin baki kawai ba tare da tabbatar da katin shiga jirgi ko wasu takardun tafiya ba.

Majiyoyi daga cikin ma'aikatar sun ce irin wannan matsala na da alaka da al'adar fifita manyan mutane, inda wasu jami'ai ke sassauta matakan tsaro ga masu fada a ji.

Ana sa ran binciken zai duba rawar da jami'an tsaron jiragen sama suka taka wajen ba da damar shiga wuraren da aka haramta a lokuta daban-daban.

Minista Keyamo ya rubuta wasika ga Trump

Mun ba ku labarin cewa Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya aika budaddiyar wasika ga Shugaba Donald Trump kan zargin kisan kiristoci.

Keyamo SAN ya bayyana cewa wannan zargi ba gaskiya ba ne domin matsalar tsaron Najeriya ta shafi kiristoci da musulmai

Hakan ya biyo bayan ci gaba da maida martani ga Shugaban Amurka, Donald Trump bayan ya yi barazanar kawo farmaki don kare kiristocin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.