"Ba a Kama Shugaban ADC Yana Cusa Daloli a Aljihu ba," Dalung Ya Wanke Ƴan APC Tas
- Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya ce an bi tsarin da ya dace wajen amincewa da ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka
- Dalung ya kare shugabannin rikon kwarya na ADC, yana mai cewa babu bidiyon David Mark da ke nuna shi yana cusa daloli a aljihunsa
- Ya jaddada cewa an nada shugabannin ne bisa tsarin doka, kuma naɗin David Mark da Aregbesola ya samu amincewar wakilan ADC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon ministan matasa da ci gaban wasanni, Solomon Dalung, ya kare sahihancin shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar 'yan hadaka, watau ADC.
Dalung ya ce, sabanin wasu shugabannin jam’iyyu, babu bidiyon David Mark, shugaban rikon kwarya na ADC, da ke nuna yana karbar rashawa.

Asali: Facebook
'Ba a kama David Mark yana cusa dala ba'
Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Lunchtime Politics na gidan talabijin din Channels a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalung ya jaddada cewa ADC ta zaɓi mutane masu kima da nagarta domin jagorantar hadakar jam’iyyun adawa, kuma kaf a cikinsu, babu mai kashin a gindinsa.
Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan hadakar, sun amince da naɗin David Mark a matsayin shugaban ADC na ƙasa, tare da Rauf Aregbesola a matsayin sakatare.
“Babu bidiyon David Mark yana cusa daloli a aljihun babbar rigarsa,” in ji Dalung, yana alakanta maganarsa da wasu shugabanni da ake zargi da karbar rashawa.
'Za a ga jagoranci na gaskiya a ADC' - Dalung
Tsohon ministan ya kuma tabbatar da cewa Ralph Nwosu, wanda ya kasance shugaban jam’iyyar ADC na baya, ya mika shugabanci ga Mark da Aregbesola bisa ka’ida.
Dalung, wanda ya yi aiki a ƙarƙashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma ya ci gaba da kasancewa cikin harkokin siyasa tun bayan barinsa ofis.
Ya ce sababbin shugabannin jam'iyyar ADC za su kawo wani sabon salo na jagoranci na gaskiya da rikon amana a siyasar adawa a Najeriya.

Asali: Facebook
‘Hadakar David Mark ba ta kwace ADC ba’ – Dalung
Tsohon ministan ya ce an bi duk matakan da suka dace wajen amincewa da jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar hadakar ’yan adawa.
Sai dai ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2023, Dumebi Kachikwu, ya zargi hadakar da kwace jam’iyyar ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.
Amma a cewar Dalung, tun watanni 18 da suka wuce ake tattaunawa kan hadakar, kuma shugabannin ADC sun san da labarin, har ma sun halarci bikin kaddamar da sabbin shugabannin.
“Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar ya halarta. Don haka ba a kwace jam’iyyar ba, domin dukkansu, 'yan ADPC da 'yan hadaka sun shaida mika mulki.
“Don haka, kalmar ‘kwace’ wata dabara ce kawai ta jan hankali a kansa. Amma a gaskiya, an bi tsarin da ya dace. Idan har shi (Kachikwu) bai da masaniya, to yana da damar ya yi tambaya."
Kalli tattaunawar a nan kasa:
Primate Ayodele ya hango makomar Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana cewa Atiku Abubakar ne za a zaɓa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar haɗaka, ADC.
Ya kuma yi gargaɗi ga jam’iyyar APC cewa za ta iya rasa mulki idan har ta ƙi bin shawarwarinsa, yana nuna damuwa kan makomar jam’iyyar mai mulki.
A gefe guda kuwa, ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya zargi ƙungiyar haɗakar da Atiku ke jagoranta da yunkurin amfani da Peter Obi domin samun ƙuri’u a zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng