Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya koma Kano Pillars, Ganduje zai bayyana shi
- Bayan jita-jita, ta tabbata Ahmad Musa ya dawo kwallo Najeriya
- Kungiyar Kano Pillars ta yi maraba da dawowar Ahma Musa gida
- Ahmed Musa ya fara rayuwar kwallonsa ne a Kano Pillars kafi ya garzaya Turai taka leda
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya kammala rattafa hannu kan kwantiragin komawa kungiyar kwallon Kano Pillars, zuwa karshen kakar 2020/2021 na NPFL.
Shugabannin kungiyar sun tabbatar da hakan a daren Litinin.
Bisa jawabin da ya fito daga ofishin shugaban kungiyar, Surajo Jambul, kuma jami'in yada labaran kungiyar, Rilwani Idris Malikawa, ya rattafa hannu, sun yanke shawaran dauko Ahmed Musa.
"Kano Pillars ta kawo karshen jita-jitan komawan kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, kungiyarta. Daga yau Talata 13/4/2021. Sai Masu Gida sun amince da siyan Ahmed Musa zuwa karshen kakar 2020/2021," Malikawa ya bayyana.
DUBA NAN: Gwamnan Edo karya yake, bamu buga N60bn don rabawa gwamnoni ba: Gwamnatin Tarayya
KU KARANTA: Gwamnan Yobe an angwance da diyar marigaryi Abacha, Hajiya Gumsu
Malikawa ya ce kungiyar ta karbi wasika daga wajen shugabannin NPFL wanda COO Salihu Abubakar yasa hannu inda suka tabbatar da cewa Ahmed Musa ya shiga kwantiragi zuwa karshen kakar.
Ya kara da cewa: "Kano Pillars na murnar maraba da Musa zuwa kungiyar kuma muna masa fatan Allah ya datar da shi."
Malikawa ya ce, amma wani sashen kwantiragin da aka rattafa hannu ya ce za'a bar Musa ya tafi duk lokacin da ya samu wani tayi daga kasar waje.
Kakakin Kano Pillars ya ce bayyan kammala komai da komai, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, zai bayyana Musa ga jama'a.
A bangare guda, Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kafa makarantun Tsangaya uku a jihar domin gwamutsa karatun almajiranci da na boko a jihar, The Punch ta ruwaito.
Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya sanar da hakan yayin rabar da kayayyakin koyarwa da kaddamar da jaridar "Teen Trust" a gidan gwamnati a Kano a ranar Talata.
Asali: Legit.ng