Dan Wasan Najeriya da Ya Kafa Tarihi, Peter Rufai Ya Rasu bayan Fama da Jinya

Dan Wasan Najeriya da Ya Kafa Tarihi, Peter Rufai Ya Rasu bayan Fama da Jinya

  • Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta yi jimami kan rasuwar tsohon mai tsaron gida, Peter Rufai, wanda ya taimaka wajen lashe gasar AFCON 1994
  • An bayyana marigayin matsayin gwarzon kwallon kafa da ya bar tarihi a Najeriya, musamman a lokacin da Najeriya ta shiga gasar cin kofin duniya na farko a 1994
  • Ƙungiyar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta tabbatar da cewa Rufai ya rasu a Lagos bayan wata jinya da ya yi, inda mutane da dama suka fara jajen rasuwar shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - An shiga jimamin rasuwar fitaccen tsohon mai tsaron ragar ƙungiyar Super Eagles, Peter Rufai, wanda aka fi sani da “Dodo Mayana.”

Rahotanni sun nuna cewa Peter Rufai ya rasu a birnin Lagos sakamakon wata jinya da ya dade yana fama da ita.

Peter Rufai yayin da ya taka leda wa Najeriya
Peter Rufai yayin da ya taka leda wa Najeriya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ƙungiyar Super Eagles ta fitar da sanarwar girmamawa da ta’aziyya a X, inda ta bayyana Peter Rufai a matsayin gwarzo a tarihin kwallon ƙafa na ƙasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin Peter Rufai a wasan kwallon ƙafa

Peter Rufai ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Najeriya a gasar cin kofin Afrika ta 1994 da kuma shiga gasar cin kofin duniya karo na farko a tarihin ƙasar.

Super Eagles ta ce Peter Rufai ya bar babban tarihi a matsayin mai tsaron raga wanda ya taka rawar gani a wasanni da dama, ciki har da gasar cin kofin duniya ta 1994 da 1998.

Haka kuma, NFF ta bayyana cewa Rufai ya rasu a Lagos ne bayan wani lokaci da ya shafe yana fama da jinya, inda sakataren NFF, Mohammed Sanusi, ya ce lamarin ya girgiza su.

Atiku da sauran 'yan Najeriya sun yi jimami

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya shiga sahun 'yan Najeriya da suka yi jimamin rasuwar Peter Rufai.

Atiku ya wallafa a X cewa:

“Ina jimamin rasuwar gwarzon mai tsaron ƙungiyar Super Eagles, Peter Rufai. Rasuwarsa babban rashi ne ga duniya da kuma harkar kwallon ƙafa.”

Atiku ya ce Peter Rufai ya bayar da gagarumar gudunmawa a harkar kwallon kafa, kuma za a ci gaba da tuna shi tare da gode masa bisa sadaukarwar da ya yi.

Masoya kwallon ƙafa daga sassa daban-daban sun rika bayyana alhini da ta’aziyya ta shafukan sada zumunta, suna tuna da irin bajintarsa a wasannin da ya wakilci Najeriya.

Peter Rufai yayin da ya samu kyauta
Peter Rufai yayin da ya samu kyauta. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kwazon Peter Rufai a ƙasashen waje

France 24 ta wallafa cewa Peter Rufai ya buga wa kungiyoyi da dama a Najeriya kafin ya fice zuwa ƙasashe kamar Benin, Belgium, Netherlands, Portugal da Spain, inda ya taka rawar gani.

Ya samu kambun bajinta yayin da Najeriya ta doke Zambia 2-1 a wasan karshe na AFCON 1994 a Tunisia.

Peter Rufai da ya rasu yana da shekara 61, ya wakilci Najeriya sau 65 a wasanni na ƙasa da ƙasa, kuma an fi saninsa da kwazo, tawali’u da kishin ƙasa.

Diogo Jota ya rasu a kasar Spain

A wani rahoton, kun ji cewa duniyar kwallon kafa ta yi rashin fitaccen dan wasa Diogo Jota a hadarin mota.

Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Portugal da ke taka leda a Liverpool ya rasu ne bayan hadari a kasar Spain.

Rasuwar Jota ta girgiza al'ummar duniya lura da cewa ya yi hadarin ne kasa da mako biyu bayan daura masa aure.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng