Siyasar Najeriya
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya sake sakin maganganu ma su zafi kan mutanen fadar shugaban ƙasa, a wannan karon ya ce ya daina yarda da su.
Ana saura kwanaki 13 gabanin babban zabe, jam'iyyar PDP a jihar Imo ta sake wayar gari cikin sabon rikici yayin da wani jigo ya fito ya fallasa kullin wasu.
Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, ya musanta kalaman gwamnan jihar, Simon Lalong, wanda ya ce tuni suka samu goyon bayan tawagar gwamnonin G5 na PDP.
Shugaban hukumar zaɓr ta kasa mai zaman kanta, Mahmud Yakubu, ya ce INEC bata tare da kowane ɗan takara ko jam'iyya, aikinta kawai ta shirya zabuka da gaskiya
Yan kwanaki kafin babban zaben kasar, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya ce lallai shine zai lashe zaben.
Primate Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya yi hasashen cewa akwai wasu tawaga daga arewa da za su hadewa Peter Obi kai don yin waje da shi.
Shugaban kwamitin amintattu na PDP ta ƙasa, Sanata Wabara, ya sanar da cewa, Wazirin Adamawa ya yi alkawarin sako shugaban IPOB a cikin kwana 100 na farko.
Mai neman zama shugaban kasa a inuwar NNPP mai kayan dadi, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce har yanzu Peter Obi na da dama guda ɗaya tal idan ya haɗa kai da shi.
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu ya yi tir da harin da wasu yan daba suka kai wa magoya bayansa a Legas.
Siyasar Najeriya
Samu kari