INEC ba ta da dan takara a babban zaben 2023, Mahmud Yakubu

INEC ba ta da dan takara a babban zaben 2023, Mahmud Yakubu

  • INEC ta kara jaddada matsayarta kan goyon bayan wanu ɗan takara ko jam'iyya a babban zaben wannan shekarar
  • Shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce INEC ba ta tare da kowane ɗan takara, aikinta ta shirya zabe
  • A ranar 25 ga watan Fabrairu da muke ciki ne za'a gudanar da zaben shugaban kasa yayin da na gwamna zai biyo baya

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta jadddada cewa ba zata goyi bayan kowane ɗan takara ko jam'iyyar siyasa ba a babban zaben 2023.

Farfesa Mahmud Yakubu, shugaban INEC na ƙasa ne ya faɗi haka yayin da yake jawabi ga ma'aikata masu kula da harkokin zaɓe (SPOs) a birnin tarayya Abuja.

Farfesa Mahmud Yakubu.
INEC ba ta da dan takara a babban zaben 2023, Mahmud Yakubu Hoto: INECNigeria
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Farfesa Yakubu ya roki su maida hankali kan rantsuwar da suka yi na kasancewa a tsakiya da bautawa Najeriya a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Fito da Gaskiya, Ya Faɗi Dama 1 Tilo da Zata Kai Peter Obi Ga Nasara a Zaben 2023

Haka zalika, ya shawarce su da karsu yi tunanin INEC zasu wa aiki, su sanya a ransu Najeriya baki ɗaya zasu yi wa aiki domin sun zama ɗaya da masu ruwa da tsaki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabinsa, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce:

"Hukumar nan ta shirya sa zaɓen 2023 ya zama zakaran gwajin dafi kuma ku ne mutanen da zasu taimaka mana mu cimma kudirinmu kuma kune zaku tabbatar da farin cikin Najeriya a ranar zaɓe."
"INEC ba jam'iyyar siyasa bace, INEC ba ta goyon bayan kowane ɗan takara, aikin mu shi ne shirya zaɓe mataki bayan mataki. Zaɓen wanda zai zama wani abu a Najeriya yana hannun yan ƙasa, su zasu yanke."

Shugaban INEC ya bayyana nauyin dake kan SPOs da aiki mai matukar daraja ga nasarar zaben 2023, sannan ya roki su rike gaskiya da amana a lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

Mako Biyu Gabanin Zaben 2023, Wasu Jiga-Jigan APC Sun Jawo Wa Tinubu Babbar Matsala

Guardiam ta rahoto Yakubu ya ci gaba da cewa:

"Ku ne mutanen da zaku kula da ma'aikatan mu na mataki mai tsada, matakin rumfunan zaɓe, nan ne kaɗai wurin da ake kaɗa kuri'a."

Atiku Ya Dau Alkawarin Sakin Shugaban IPOB Idan Ya Ci Zabe, Wabara

A wani labarin kuma Ɗan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sakin shugaban yan ta'adda idan ya ci zaɓen 2023

Shugaban kwamitin amintattun PDP, Sanata Wabara, ya ce Wazirin Adamawa ya daukar masu alkawarin sako Nnamdi Kanu a kwana 100 na farko.

Bayanai sun nuna cewa tun shekarar da ta gabata, mahukunta a Najeriya ke rike da Kanu, shugaban IPOB bisa tuhumar hannu a aikata ta'addanci a kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel