Yan Bindiga Sun Harbi Shugaban PDP Na Gunduma a Jihar Imo

Yan Bindiga Sun Harbi Shugaban PDP Na Gunduma a Jihar Imo

  • Yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kutsa har ƙuryan cikin gida sun harbi shugaban PDP a gundumar Ogbaku, jihar Imo
  • Rahotanni sun bayyana cewa ɗan siyasan ya shiga gida da misalin ƙarfe 9:00 na dare ba tare da sanin maharan sun yi wa gidansa tsinke ba
  • Jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sandan jihar ya ce a yanzu sun fara bincike don kame masu hannu a harin

Imo - Wasu miyagun 'yan bindiga sun harbi shugaban Peoples Democratic Party (PDP) na gundumar Ogbaku, ƙaramar hukumar Mbaitolu ta jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa ɗan siyasan mai suna, Charles Oke, an harbe shi ne a gidansa da ke yankin Umunomo Nsokpo ranar Asabar da daddare.

Matsalar tsaro a Najeriya.
Yan Bindiga Sun Harbi Shugaban PDP Na Gunduma a Jihar Imo Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi kwantan ɓauna a gidan shugaban PDP, wanda ya dawo gida ba tare da sanin tuggun da aka ƙulla masa ba da karfe 9:00 na dare.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Kwana 13 Gabanin Zabe, An Nemi Kuɗin Kamfen Atiku An Rasa, Jigon PDP Ya Tona Masu Hannu

Wasu majiyoyi daga yankin da abun ya faru sun ce 'yan bindigan sun harbi Mista Oke a ƙafafuwansa. Kum sun samu shiga gidan ta katanga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar majiyoyin tuni aka garzaya da mutumin zuwa Asibitin da ba'a baygana ba domin kula da lafiyarsa.

Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama's na jam'iyyar PDP a jihar Imo, Collins Opuruozor, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai da safiyar Litinin.

Mista Opuruozor, ya ce PDP na kan bincike kan abinda ya faru kuma ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba jam'iyya zata fitar da cikakken bayani game da harin.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda reshen Imo, Henry Okoye, ya ce dakarun yan sanda sun fara binciken gano maharan da kuma damƙe su, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mutane 15 Sun Jikkata Yayin da 'Yan Daba Suka Kai Hari Gidan Ɗan Majalisar PDP, An Gano Masu Hannu

"Mun kara tsananta sintiri a yankin da nufin dakile yunkurin sake kai sabon hari," inji Mista Okoye, mataimakin Sufuritandan yan sanda.

A wani labarin kuma 'Yan Daban PDP Sun Yi Garkuwa da Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Ribas

Rahotanni daga jihar sun nuna cewa an ji karar harbe-harben bingigu da yankin da lamarin ya faru, kuma wani ganau ya turo bidiyon halin da ake ciki.

Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da yan daba ke kai hari wuraren kamfe su ci karensu babu babbaka ba a jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262