Peter Obi Ya Bayyana Wadanda Suka Kai Wa Magoya Bayansa Hari A Legas

Peter Obi Ya Bayyana Wadanda Suka Kai Wa Magoya Bayansa Hari A Legas

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, ya soki harin da aka kai wa magoya bayansa a Legas inda aka rahoto rahoto an raunata yan Obidient hudu
  • Mai fatan zaman shugaban kasar ya zargi shugabannin siyasa wadanda ke furta maganganu na tunzura magoya bayansu kai wa yan jam’iyyun adawa hari
  • A cewar Obi, ya kamata hukumomin tsaro su tabbatar an kama wadanda suka kai harin kuma an hukunta su

TBS, Legas - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya zargi shugabannin siyasa masu furta kalaman ‘tunzura’ al’umma a matsayin wadanda suka janyo harin da aka kai wa magoya bayansa yayin ralli na shugaban kasa a Legas.

An rahoto cewa an kai wa wasu magoya bayan tsohon gwamnan na Jihar Anambra hari a ranar 11 ga watan Fabrairu, yayin da suke kan hanyarsu na zuwa gangamin dan takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Kwankwaso Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka Idan An Zabe Shi Shugaban Kasa

Obi da Datti
Peter Obi Ya Bayyana Wadanda Suka Kai Wa Magoya Bayansa A Legas. Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da Peter Obi ya ce game da harin da aka kai wa magoya bayansa a Legas

Awanni bayan rahoton, wanda ta yi wu an shirya kai wa ko ba haka ba, Obi ya tafi shafinsa na Twitter ya yi tir da harin kuma ya dora alhakin kan shugabannin da ke furta maganganu na dumama siyasa.

Mai fatan zaman shugaban kasar daga nan ya yi Allah wadai ta yawaita hare-haren da ake yawan kai wa yan jam’iyyar adawa, ya kara da cewa Najeriya da ya ke fatan ginawa za ta ginu kan zaman lafiya da adalci ne da girmama dokar kasa.

Abin da ke faruwa kan Peter Obi, Jam’iyyar Labour, Gangamin Legas, Zaben 2023

Daga nan Obi ya yi kira ga gwamnatin Jihar Legas da jami’an tsaro su tabbatar an Kano wadanda suka kai harin sannan a hukunta su.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

Ya ce:

“Ba za mu amince hare-hare da jam’iyyun hamayya ke kai wa magoya bayan mu ba, kuma galibi kalaman tunzura da shugabannin siyasa ke yi ke janyo hakan. Sabuwar Najeriya da muke nema za ta ginu ne kan zaman lafiya, adalci da girmama doka.”

Ga rubutun da ya yi a Twitter a nan kasa:

Ku amshi kudin wasu yan siyasa amma kada ku zabe su, Peter Obi ya shawarci yan Najeriya

A wani rahoton kun ji cewa mai neman kujerar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar Labour, Peter Obi ya shawarci magoya bayansu su karbi kudin yan siyasa amma su zabe shi.

Ya yi wannan jawabin ne yayin ralli dinsa a birnin Ilorin jihar Kwara, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164