Rigimar PDP: Tawagar Gwamnonin G-5 Ba Su Goyon Bayan Bola Tinubu, Jang

Rigimar PDP: Tawagar Gwamnonin G-5 Ba Su Goyon Bayan Bola Tinubu, Jang

  • Tsohon gwamnan Filato, Jonah Jang, ya musanta kalaman Lalong cewa G-5 sun koma bayan Bola Ahmed Tinubu
  • Mista Jang, mamba a tawagar G-5 karkashin Wike, ya ce DG na kamfen APC mafarki kawai yake yi da tsakar rana
  • Gwamnonin guda 5 na jam'iyyar PDP sun raba gari da shugabancin jam'iyya kan kujerar Dakta Iyorchia Ayu

Plateau - Mamban tawagar gaskiya G-5 kuma tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, ya musanta ikirarin Darakta Janar na kwamitin kamfen APC, Gwamna Simon Lalong.

Rahoton jaridar Punch ya ce Jang ya karyata kalaman Lalong cewa tawagar G-5 ƙarƙashin jagorancin gwamna Nyesom Wike, suna goyon bayan Bola Tinubu.

Lalong da Jonah Jang.
Rigimar PDP: Tawagar Gwamnonin G-5 Ba Su Goyon Bayan Bola Tinubu, Jang Hoto: punchng

Da yake martani a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakinsa, Clinton Garuba, ranar Lahadi, tsohon gwamnan ya ce 'yan Najeriya sun jima da dawowa daga rakiyar gwamna Lalong.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Ya Fusata, Ya Umarci a Kama Duk Wanda Ya Ƙi Karban Tsoffin Kuɗi

Sanarwan ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Alama ta zahiri dake nuna Lalong mafarki yake shi ne tunanin gwamnonin PDP na tawagar G-5 da makusantansu haɗi da tsohon gwamna Jang suna goyon bayan Tinubu."
"Sun nanata cewa ba su matsala da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, damuwarsu hanyar da aka bi aka miƙa masa takara. Eh gaskiya ne tawagar gaskiya ta samu saɓani da PDP kuma ta janye daga kamfen Atiku."
"Amma hakan ba yana nuna suna goyon bayan ɗan takarar jam'iyyar APC bane. Lalong ne kaɗai da masu mafarki kamarsa su ke tunanin haka."

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa gwamnonin G-5 da suka fusata da abinda ke faruwa a PDP sun kunshi Samuel Ortom (Benue), Ifeanyi Ugwanyi (Enugu), Okezie Ikpeazu (Abia) da Seyi Makinde (Oyo).

Karƙashin jagorancin Nyesom Wike na jihar Ribas, gwamnonin sun ja daga da shugabancin PDP kan tsarin raba manyan mukaman jam'iyya, sun bukaci Ayu ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Hadarin Mota ya Rutsa ‘Dan takaran Gwamna da Shugaban Jam’iyyar APC a Titi

INEC ba ta da dan takara a babban zaben 2023, Mahmud Yakubu

A wani labarin kuma Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta jaddada cewa babu ɗan takarar da take goyon baya a babban zaben 2023

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce suna tsakiya kuma abinda suka maida hankali shi ne gudanar da zabe kamar yadda doka ta tanadar.

Farfesa Yakubu ya roki SPOs da su gaskiya a al'amuran aikinsu domin sunr tushe gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel