Sheikh Pantami Ya Karbi Shaidar Takarar Gwamnan Jihar Gombe a Babban Zaben 2027
- Jam'iyyar adawa ta PDP ta mika wa Farfesa Isa Ali Pantami takardar shaidar zama ɗan takarar gwamnan Gombe a zaben 2027
- An bai wa 'yan takarar gwamnan PDP takardun shaida ne a taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na jam’iyyar a Abuja
- Shugaban tsagin PDP da ke biyayya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, Abdulrahman Mohammed, ne ya jagoranci taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria – Jam’iyyar PDP ta mika takardar shaidar takara ga tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Damani, Farfesa Isa Ali Pantami, a matsayin dan takarar gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.
Pantami ya karbi takardar ne ranar Laraba yayin taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) da kuma rantsar da sababbin mambobin NEC na jam’iyyar a hedkwatar PDP da ke birnin Abuja.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta tattaro cewa taron ya gudana karkashin jagorancin shugaban tsagin PDP, Abdulrahman Mohammed, wanda ke biyayya ga ministan Abuja, Nyesom Wike.
Tsagin PDP ya gudanar da taron NEC
Rahotanni sun nuna cewa shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP daga sassan kasar nan daban-daban sun halarci taron NEC yau Laraba, 24 ga watan Yuni, 2026.
An tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi makomar jam’iyyar PDP da kuma shirye-shiryenta gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A cewar tsagin jam’iyyar PDP, taron ya kasance wani muhimmin mataki na ƙarfafa tsarin shugabanci da kuma tabbatar da shirye-shiryen tunkarar zaɓuka masu zuwa.
PDP ta fitar da 'yan takarar gwamna
A yayin taron, jam’iyyar PDP ta mika takardun shaidar takara ga wasu daga cikkn ‘yan takarar gwamna da aka amince da su tare da wallafa sunayensu a hukumance.
Matakin ya tabbatar da su a matsayin zababbun ‘yan takarar PDP a jihohinsu domin tunkarar babban zaben 2027.

Kara karanta wannan
2027: Ana zargin goyon bayan Sheikh Pantami ya jefa kamfanin Gombawa Motors a matsala
Isa Pantami ya karbi takardar shaida
Sheikh Isa Ali Pantami, wanda shi ne tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, na cikin wadanda suka samu wannan takarda a taron, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Sakamakon karbar wannan takardar, Pantami ya zama dan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP kamar yadda jam’iyyar ta sanar a wajen taron.

Source: Facebook
Magoya bayan malamin a ciki a wajen jihar Gombe sun nuna farin cikinsu da wannan mataki, inda suka ce da ikon Allah Pantami ne gwamna na gaba.
Muhammad Ahmad, wani mai goyon bayana Pantami a Gombe, ya shaisa wa Legit Haisa cewa al'ummar jihar sun shirya kada wa malam kuri'unsu a zaben 2027.
"Wannan wata alama ce da ke tabbatar da takarar Malam, wasu na yada cewa ai PDP yan takara biyu ta tsaida a Gombe, to wace PDP din? Mu Malam kadai muka sani."
"Za mu bada karfinmu, lokacinmu da dukiyarmu wajen tabbatar da nasarar Malam idan Allah ya yarda," in ji shi.
Pantami ya kara samun goyon baya
A wani rahoton, kun ji cewa wani tsohon mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Gombe , Aliyu Musa, ya yi murabus daga jam'iyyar APC mai mulki, inda ya koma PDP.
Aliyu Musa ya koma jam'iyyar PDP ne tare da dubban magoya bayansa, a wani mataki da zai ƙara sauya yanayin siyasa gabanin zaɓen gwamnan jihar Gombe.
Tsohon hadimin gwamnan ya ce shawararsa ta barin APC ta samo asali ne daga goyon bayan da yake ba wa burin takarar gwamna na tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Asali: Legit.ng

