Za a Hade Maka Kai a Arewa: Primate Ayodele Ga Peter Obi

Za a Hade Maka Kai a Arewa: Primate Ayodele Ga Peter Obi

  • An bukaci Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ya yi hankali don wasu daga arewa za su hade masa kai yayin babban zaben kasar
  • Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ne ya yi hasashen a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu
  • Malamin addinin wanda ya kuma nuna tsoro kan amfani da na'urar BVAS sannan ya yi hasashen cewa wasu jami'an INEC za su yi kutse a tsarin

Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya aika sakon gaggawa ga dan takarar shuganan kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.

A hasashensa wanda hadimin labaransa, Osho Oluwatosin ya saki a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu, Ayodele ya ayyana cewa ana iya hade masa kai daga yankin arewa.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Fani-Kayode Ya Bayyana Abin Da Zai Faru Da Kiristoci Idan Obi Ya Fadi Zabe

Primate Ayodele da Peter Obi
Za a Hade Maka Kai a Arewa: Primate Ayodele Ga Peter Obi Hoto: INRI Evangelical Spiritual Church, Mr. Peter Obi
Asali: Twitter

Malamin addinin ya bayyana cewa yawanci arewa ce ke yanke hukunci kan wanda zai zama shugaban kasa yayin babban zaben kasar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Kuri'un Arewa ne zai tabbatar da wanda zai zama shugaban kasar Najeriya, ya zama dole Obi ya yi a hankali don kada kuri'un arewa ya yi waje da shi.
"Za a masa taron dangi kan kuri'un da zai samu a arewa. Ba za a yi juyin mulki ba a Najeriya, Allah bai yarda da hakan ba a kasar."

Na hango siddabaru a INEC - Primate Ayodele

Da yake ci gaba da jawabi, Primate Ayodele ya yi zargin cewa akwai wani abu da ya kira da siddabaru a hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), kuma ya nuna damuwarsa kan tsarin tura sakamakon zaben 2023 ta na'ura da BVAS.

Kara karanta wannan

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

Malamin addinin ya ce wasu jami'an INEC za su yi kutse a tsarin kuma cewa wasu mutane za su yi kokarin kawo tangarda wajen nasarar zaben, rahoton Daily Post.

Kalamansa:

"Ya zama dole INEC ta tashi tsaye a zaben nan, za a yi wasan siddabaru da dama a hukumar. Na damu da tsarin tura sakamakon zabe da lamarin BVAS na INEC."

Ba mai samun kaso 70 na kuri’un Arewa cikin yan takara a 2023, Yakassai

A wani labarin, Tanko Yakassai ya yi hasashen cewa babu wanda zai samu kaso 70 cikin dari na kuri'un yan arewa cikin masu neman takarar kujerar shugaban kasa a 2023.

Yakassai wanda ya ce za a yi raba daidai kuri'un tsakanin yan takara, ya ce Bolka Tinubu na APC ne zai lashe zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel