Ban Aminta da Shugabancin Mutanen Dake Kewaye da Buhari Ba, El-Rufai

Ban Aminta da Shugabancin Mutanen Dake Kewaye da Buhari Ba, El-Rufai

  • Gwamna Malam Nasiru El-Rufai, ya kara sakin maganganu kan mutanen fadar shugaban kasa ana shirin zaben 2023
  • A kwanakin baya an ji gwamnan na zargin wasu mutane a kewayen Buhari da ke yakar Bola Tinubu
  • Kalaman gwamnan sun haddasa cece-kuce a jam'iyya mai mulki inda aka ji wasu na goyon bayansa

Kaduna- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya sake sakin kalamai masu ɗumi yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zabe a watan da muke ciki.

Rahoton jaridar Daily Trust ya tattaro cewa a 'yan kwanakin nan El-Rufa'i ya haddasa kace-nace musamman kalamansa kan tsarin sauya fasalin naira da CBN ya tsiro da shi.

Gwamna El-Rufai
Ban Aminta da Shugabancin Mutanen Dake Kewaye da Buhari Ba, El-Rufai Hoto: Malam Nasiru
Asali: UGC

Gwamnan ya namaye kanun labarai musamman lokacin da ya ce akwai wasu, "'yan kanzagi a fadar shugaban kasa," da ke yakar ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Bola Tinubu a Villa, Bayanai Sun Fito

Na daina yarda da nagartar mutanen dake kewaye da Buhari - El-Rufai

A wata hira da jaridar Premium Times ta bayan fage, gwamnan Kaduna ya ce a yanzu ya daina aminta da nagartar jagorancin mutanen da ke kewaye da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Na aminta da Buhari, kuma har yau na yarda da shi ba zan daina ba amma waɗanda ke kewaye da shi na daina amanna da su, bana aminta da matakin da suka ɗauka ko wani aiki da ya fito daga gare su."

- A cewar Malam Nasiru El-Rufai.

Akwai masu adawa da Tinubu a Villa - Gwamna Kaduna

Idan baku manta ba a cikin shirin Channels tv a farkon watan nan, Gwamnan ya ce wasu mutane sun shiga rigar Buhari suna kokarin cimma wata manufa saboda wanda suka so ya sha kaye a zaben fidda gwanin APC.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Muna Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira Da Sharadi 1: Majalisar Magabata

"Na yi imani cewa akwai wasu mutane a fadar shugaban kasa da suke fatan mu faɗi zaɓe saboda ba su samu abinda suke so ba. Suna da nasu ɗan takara amma bai yi nasara a zaben fidda gwani ba."
"Suna ta kulla-kullan yadda zasu ga mun sha kaye a zaɓe kuma suna nan sun ɓuya a bayan shugaban kasa suna angiza shi ya yi abinda yake ganin ya dace."

A wani labarin kuma Ganduje Ya Rufe Kantin Siyayya a Jihar Kano Saboda Kin Karbar Tsoffin Kudi

Gwsmnatin Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta umarci a garkame babban kantin sayayya Wellcare bisa gano sun daina karban tsoffin naira.

Ta hannun hukumar kula da hakkin masu sayayya, geamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne bisa umarnin gwamna kuma ta gargaɗi sauran 'yan kasuwa su tuna har yanzu ba'a haramta amfani da tsohon naira ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel