Tinubu Ne Zai Lashe Zabe a Shiyyar Arewa Maso Yamma da Gagarumin Rinjaye, Inji Jigon APC Salihu Lukman

Tinubu Ne Zai Lashe Zabe a Shiyyar Arewa Maso Yamma da Gagarumin Rinjaye, Inji Jigon APC Salihu Lukman

  • Wata sanarwa da jigon APC ya fitar ta ce, Tinubu ne zai yi nasara a zaben 2023 a yankin Arewa maso Yamma
  • Hakazalika, ya bayyana yakinin cewa, dukkan kujeru a jihohin shiyyar za su zama mallakin APC a zaben bana
  • Ya yi kira ga matasa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su ci gaba da gangamin tallata jam’iyyar

Jam’iyyar APC a Arewa maso Yammacin Najeriya ta ce tana da kwarin gwiwar cewa, dan takararta na shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai yiwa zaben 25 ga watan Faburairu cin kaja a shiyyar.

Arewa maso Yamma ta hada jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara, kuma su kadai kuri’u miliyan 22.67 suka mallaka, TheCable ta ruwaito.

A cikin wata sanarwar da Salihu Lukman, mataimakin shugaban APC na kasa (shiyyar Arewa maso Yamma) ya fitar ya ce, yadda gangamin APC ke tafiya da kuma tasirin shugabannin APC nuni NE ga nasarar Tinubu a zaben bana.

Kara karanta wannan

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

Tinubu zai yi tasiri a Arewa maso Yamma
Tinubu Ne Zai Lashe Zabe a Shiyyar Arewa Maso Yamma da Gagarumin Rinjaye, Inji Jigon APC Salihu Lukman | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa, Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a jihohin Arewas maso Yamma saboda karbuwar APC da tasirinta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alamu sun nuna APC za ta yi nasara a dukkan matakai, inji Salihu Lukman

A cewarsa:

“Dukkan wadannan alamomi ne na nasara ga APC a Arewa maso Yamma ga dan takararmu na shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben 25 ga watan Faburairun 2023, da ma dukkan ‘yan takara a matakin majalisar kasa.
“Har ila yau alamomin nasara ne ga ‘yan takarar gwamna da majalisun jihohi a dukkan jihohi bakwai na Arewa maso yamma.
“Muna da yakinin cewa da yardar Allah dukkan jihohin bakwai a Arewa maso Yamma, har da Sokoto za su zama jihohin APC a ranar 29 ga watan Mayu."

Ya yi kira ga dukkan mambobin majalisar kamfen na APC a shiyyar da su hada kai da shugannin jam’iyyar a matakai na kasa da sama don tabbatar da nasararta a zaben bana, rahoton BluePrint.

Kara karanta wannan

Ina son gaje kujerar Buhari: Tinubu ya nemi goyon bayan sarkin Musulmi, sarkin ya ba shi amsa

Dan takawar gwamnan LP ya koma APC

A wani labarin kuma, kunji yadda dan takarar gwamna a jam'iyyar Labour ya sauya sheka zuwa APC.

Wannan na fitowa ne bayan da ya yi wata ganawa da dan takarar shugaban kasan APC, Bola Ahmad Tinubu.

Ya kafa hujja da cewa, jam'iyyar Labour ba ta damawa da 'yan Arewa wajen yanke shawarin da ya dace a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel