Bidiyo: An Kama Jami'in Ƴan Sandan Najeriya Yana Kwankwadar Barasa a bakin Aiki
- Wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna wani jami’in ‘yan sanda yana shan abin da ake zargi barasa ce yayin da yake aiki
- Jama’a sun yi Allah-wadai da lamarin tare da neman a dauki mataki idan aka tabbatar da cewa jami’in d'an sanda ya aikata laifi
- Bayan bullar bidiyon da ce-ce-ku-cen jama'a, rundunar ‘yan sanda ta ce ta fara bincike domin gano jami’in da wurin da abin ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara bincike kan wani da ake zargin jami'inta ne, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, da aka gani a bidiyo yana kwankwadar barasa.
Wani bidiyo ya nuna lokacin da jami'in yake tultular barasa yayin da yake gudanar da aikin binciken ababen hawa a hanya.

Source: Twitter
Bidiyon d'an sanda ya jawo cece-kuce
Bidiyon, wanda ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, ya nuna jami’in yana hulda da mutanen da ke cikin wata mota da aka tsayar yayin binciken hanya, a cewar rahoton Tribune.
A cikin bidiyon, wanda wani daga cikin wadanda ke a motar yake dauka, an ga jami’in yana daga kwalbar yana sha sau da dama yayin da ake ci gaba da aikin binciken.
Haka kuma, an ji shi yana fadin wasu lambobi yayin da daya daga cikin mutanen da ke cikin motar ke amfani da waya, lamarin da ya sa wasu ke zargin yana neman kudi ba bisa ka’ida ba.
Wannan ya jawo cece-kuce daga jama’a da dama, inda wasu suka nemi a dauki matakin ladabtarwa kan jami'in idan har aka tabbatar ya aikata laifi.
Abin da dokar ‘yan sanda ta tanada
Idan aka tabbatar da cewa jami’in ya sha giya yayin aiki, hakan zai saba wa tanadin sashe na 100(1) na dokar aikin d'an sanda ta 2021.
Dokar ta hana jami’an ‘yan sanda shan giya ko amfani da wasu abubuwan maye ko kara kuzari yayin da suke bakin aiki.
Dokar ta ce:
“Yayin da yake bakin aiki, jami’in ‘yan sanda ba zai sha wani abin maye, ko amfani da sinadarai masu canza yanayi ba; idan ya yi hakan, za a hukunta shi bisa tsarin ladabtarwa na rundunar.”
Rundunar ta fara bincike
Da take martani kan bidiyon, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce tana sane da lamarin kuma ta fara kokarin gano jami’in da ake magana a kai.

Source: Twitter
Jami’in yada labarai na zamani na rundunar, Aliyu Giwa, ya ce shugabancin rundunar ya fara bincike domin gano inda abin ya faru da kuma hakikanin abin da ya faru.
A shafinsa na X, Aliyu Giwa ya ce:
“Rundunar tana sane da wani bidiyo da ya yadu wanda ke zargin wani jami’in ‘yan sanda yana neman wata alfarma ta kudi tare da shan abin da ake tunanin giya ce yayin hulda da mutanen da ke cikin mota.”
Kalli bidiyon jami'in a kasa:
'Dan sanda ya kashe wani a maye
A wani labari, mun ruwaito cewa, an shiga fargaba da wani jami’in ‘yan sanda ya kashe mutum ɗaya a yankin Maitumbi da ke jihar Neja, bayan ya sha giya da ya bugu.
Majiyoyi sun ce jami’in da ake zargi yana aiki ne a ofishin ‘yan sanda na Maitumbi, ya shiga harbin ba ji ba gani bayan buguwarsa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja ya ba da umarnin fara bincike kan lamarin, yayin da ake neman jami'in da ya yi kisan ruwa a jallo.
Asali: Legit.ng