Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar Labour Ya Sauya Sheka Zuwa APC

Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar Labour Ya Sauya Sheka Zuwa APC

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, dan takarar gwamna a jam'iyyar Labour, Bashir Ishaq Bashir ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
  • A baya dan takarar ya yi watsi da taron gangamin LP da aka gudanar a jihar Kano a watan Janairun da ya gabata
  • Ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasan APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu lokacin da suka gana a Legas

Jihar Kano - Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar Labour, Bashir Ishaq Bashir ya bayyana sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, Punch ta ruwaito.

Wannan sauya sheka mai ban mamaki na zuwa da yammacin ranar Lahadi 12 ga watan Faburairun 2023.

A ranar 21 ga watan Janairu, dan takarar gwamnan ya kauracewa taron ganganin dan takarar shugaban kasa da jam'iyyar ta Labour ta gudanar a Kano.

Kara karanta wannan

Karya Ne, Babu Wanda Ya Yiwa Mai Mala Buni Rajamu: Ahmad Lawan

Dan takarar Labour a Kano ya koma APC
Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar Labour ya sauya sheka zuwa APC | Hoto: Engr. Bashir Ishaq Bashir - Hasken Kanawa
Asali: Facebook

Sauran wadanda suka kauracewa taron gangamin jam'iyyar sun hada da daraktan kamfen Obi na Kano, Mohammed Zarewa, kodinetan kamfen na jihar, Balarabe Wakili da Idris Dambazau, wani jigon jam'iyyar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalilin sauya shekar dan takarar

Wata majiya ta kusa da ta tabbatar da sauya shekan dan takarar ta ce, ya bar LP ne bisa zargin an mai da masu ruwa da tsaki na Arewa saniyar ware a jam'iyyar.

A cewar majiyar, ana ware manyan Arewa na jam'iyyar kan shawarin da ake yankewa duk da kuwa yana da alaka da shiyyar.

Bayan sauya shekan, an ce wasu daga jiga-jigan jam'iyyar sun gana da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, rahoton Daily Trust.

Sai dai, wani rahoton Daily Nigerian ya ce, dan takarar gwamnan ya gana da Tinubu a Legas, kuma ya bayyana masa goyon bayansa a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Matasan APC sun yiwa Gwamna Mai Mala Buni rajamu a Yobe

Kwamishinan Kasafin Kudin Jihar Zamfara Ya Bar APC Ya Koma PDP

A wani labarin kuwa, kwamishinan kasafin kudi a jihar Zamfara ya bayyana sauya sheka zuwa PDP a makon jiya.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyun siyasa a Najeriya ke ci gaba da shiri tare da zage dantse wajen ganin nasara a zaben bana.

Ya bayyana cewa, ya bar jam'iyyar APC ne saboda gazawarta wajen shayar da jama'a romon dimokradiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel