An Fara: An Bayyana Motocin Alfarma domin Tallata Tinubu a 2027

An Fara: An Bayyana Motocin Alfarma domin Tallata Tinubu a 2027

  • Cubana Chief Priest ya fitar da motocin da aka sanya wa hotunan yakin neman zaɓen shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 mai zuwa
  • Legit Hausa ta gano cewa an sanya hotunan Tinubu, Kashim Shettima da Seyi Tinubu tare da tambarin jam'iyyar APC a jikin motocin
  • Fitar da motocin ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sadarwa, inda wasu suka soki lamarin saboda yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Fitaccen ɗan kasuwa kuma mai harkokin nishaɗi, Pascal Okechukwu, wanda aka fi sani da Cubana Chief Priest, ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.

Ya jawo rudani ne bayan ya nuna wasu motocin alfarma da aka yi wa kwalliyar yakin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi maganar da ta ba da mamaki kan tsaro

Motocin tallan Bola Tinubu a 2027
Motocin da ala fitar domin tallata Tinubu/Shettima a 2027. Hoto: @cubana_chiefpriest
Source: Instagram

An fitar da motocin tallan Tinubu

A cikin wasu bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, ya nuna wata mota kirar Lamborghini Urus da kuma wata mota kirar Dongfeng M-Hero da aka ajiye a wani gida.

An yi wa motocin kwalliya da launukan kore, fari, shuɗi da ja, tare da sanya hotunan shugaba Tinubu, Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu.

Haka kuma an rubuta kalmomi kamar "City Boy Movement", "APC" da sauransu a jikin motocin tallata shugaban kasar domin neman tazarce.

Martanin jama'a kan motocin

Bidiyon, waɗanda daga baya wasu mutane suka sake wallafawa a sauran shafukan sada zumunta, sun jawo martani daban-daban, musamman a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan zaben 2027.

Wani mai amfani da shafin X mai suna Fowobio ya rubuta cewa:

"Duba yadda ake amfani da kuɗin da za a iya inganta rayuwar al'umma da shi wajen."

Kara karanta wannan

2027: Hadiman Tinubu za su shigo wasu jihohin Arewa jin ra'ayoyin talakawa

Wani mai suna Chukwu Ebuka kuwa ya ce:

"Mutumin nan neman kudi kawai ya ke. Son kuɗi shi ne tushen dukkan sharri."

Obi Ofala ya ce:

"Wannan bai damu da abin da mutane ke faɗa ba. Abin da yake nema shi ne samun kusanci da masu iko."
Shugaban Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasar Bola Tinubu a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Cubana Chief Priest, wanda ake cewa shi ne daraktan ƙungiyar City Boy Movement a jihar Imo, ya dade yana bayyana ra'ayinsa kan siyasa da kuma goyon bayansa ga jam'iyyar APC.

Sai dai Cubana Chief Priest bai fitar da wani karin bayani game da hotunan da ya fitar ba a daidai lokacin hada wannan rahoton.

'Tinubu ya samu karbuwa' Onanuga

A wani labarin, mun kawo muku cewa hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa har yanzu Bola Tinubu yana samun karbuwa.

Ya yi magana ne yayin da ya ce sun ziyarci wasu jihohi a Kudu maso Gabas na Najeriya domin jin ra'ayoyin jama'a game da mulkin Tinubu.

Bayan ya ce sun samu karbuwa a jihohin Kudu, Onanuga ya ce za su nufi wasu jihohin Arewa maso Yamma domin jin ra'ayoyin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng