Atiku Ya Dau Alkawarin Sakin Shugaban IPOB Idan Ya Ci Zabe, Wabara

Atiku Ya Dau Alkawarin Sakin Shugaban IPOB Idan Ya Ci Zabe, Wabara

  • Shugaban BoT-PDP, Sanata Wabara, ya ce Atiku Abubakar, ya ɗauki alkawarin sako musu ɗansu idan ya ci zabe mai zuwa
  • A wurin ralin shugaban kasa na jihar Abiya, Wabara ya ce Atiku zai sako jagoran kungiyar IPOB idan ya hau mulki
  • Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, na tsare a hnnun mahukunta tun bara

Abia - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin sako Nnamdi Kanu, idan Allah ya ba shi mulki a zaben wannan watan da muke ciki.

Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar 'yan aware (IPOB) na tsare a hannun hukumomi a Najeriya tun shekarar da ta gabata, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Atiku da Nnamdi Kanu
Atiku Ya Dau Alkawarin Sakin Shugaban IPOB Idan Ya Ci Zabe, Wabara Hoto: channels
Asali: UGC

Amma shugaban kwamitin amintattu (BOT) na PDP ta ƙasa, Sanata Adolphus Wabara, ya yi ikirarin cewa wazirin Adamawa ya musu alkawarin sako jagoran IPOB a cikin kwanaki 100 na farko idan ya hau mulki.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tsage Gaskiya, Ya Faɗi Ɗan Takarar Shugaban Kasan Da Zai Iya Cin Zaben 2023

Sanata Wabara ya yi wannan furucin ne a wurin ralin kamfen shugaban kasa na PDP wanda ya gudana a Umuahia, babban birnin jihar Abiya ranar Asabar 11 ga watan Fabrairu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban BoT-PDP ya ce:

"Atiku ya yi alkawarin sako mana ɗanmu daga gidan gyran hali a cikin kwanaki 100 na farko da kafa gwamnatinsa. Ba ya jin tsoron kowa kuma zai cika alƙawarin da ya ɗauka."

Wabara, tsohon shugaban majalisar dattawa ya roki masu kaɗa kuri'a a jihar Abiya su jefa wa ɗan takarar shugaban kasa na PDP kuri'unsu a zaen 25 ga wata.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Atiku ya halarci wurin ralin tare da abokin gaminsa, Gwamna Okowa na jihar Delta, da shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu.

Sauran waɗanda ke tawagar wazirin Adamawa sun kunshi gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel, da gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Sarkin Musulmi Abu 3 da Suka Sa Ya Shiga Kamfen Tinubu

Dama Daya Tal Peter Obi Ke Da Ita Ya Hada Kai NNPP, Kwankwaso

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Kano ya bayyana abu 1 da ya ragewa Peter Obi idan yana son shiga fadar shugaban kasa a 2023

Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwa NNPP, Rabiu Kwankwaso, yace Obi ba zai kai labari ba matukar bai zo sun haɗa kai ba.

Kwankwaso, ya kuma yi fatali da zabukan gwajin da wasu kungiyoyi ke shiryawa a Intanet, ya ce ya zarce kason da ake ba shi a arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel