Siyasar Najeriya
Gwamnan jihar Zamfara, Lawal Dauda, ya bayyana yadda tsohuwar gwamnatin Matawalle ta siyo manyan motoci na alfarma na biliyan N2.79bn amma ko ɗaya bai bari ba.
Tsohon gwamnan jihar Ribas wanda ya sauka ranar Litinin da ta shige, Nyesom Wike, ya ce ko kaɗan bai fara tunanin sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC ba.
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya zargi jam'iyyar APC a jihar Ƙaduna da rashin iya gudanar da mulki, a shekara takwas da ta kwashe a mulkin jihar.
Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na bukatar goyon bayan kowane ɗan Najeriya a daidai wannan lokaci mai matuƙar wahala.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta tabbatar wa Kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamnan Kaduna cewa Malam Uba Sani ne ya samu nasara a watan Maris.
Gwamnonin ci gaba na jam'iyyar APC sun nuna damuwarsu kan yadda yan kasuwa suka ƙara farashi nan take bayan kalaman sabon shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sanar da nadin George Akume, tsohon ministan Ayyukan Na Musamman a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya a gwamnatinsa
Daga karshe, Shugaba Tinubu, ya tabbatar da nadin Femi Gbajabiamila, Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya a matsayin, shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa.
Kotun sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da nasarar da dan takarar Gwamna a jihar Oyo karkashin jam'iyyar PDP Seyi Makinde ya yi a zaben 2023 da ya gabata.
Siyasar Najeriya
Samu kari