An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

  • Jami'an tsaro sun harbe tsohon kansilan Getso da ke karamar hukumar Gwarzo har lahira bisa zargin yunkurin satar akwatun zabe
  • Makusantan mamacin sun bayyana cewa ba zai yiwu ace ya je satar kuri'a ba, yayin da aka gaza jin ta bakin jami'an tsaro kan mutuwar tsohon kansilan ba
  • Akwai rahotannin lalata kuri'a a sassa daban daban na fadin Jihar Kano, yayin da jami'an tsaro ke cigaba da kokarin saita al'amura

Jihar Kano - An bindige tsohon kansila na gundumar Getso, Ibrahim Nakuzama, har lahira kan zargin sace akwatin zabe.

Daily Trust ta rahoto cewa jami'an tsaro ne suka bindige shi a karamar hukumar Gwarzo ta Kano a ranar Asabar.

Tsohon Kansila
An Bindige Tsohon Kansila A Kano Kan Zargin Sace Akwatin Zabe. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Lamarin ya faru ne yayin da ake gudanar da zabukan gwamnoni da yan majalisan jiha a jihar ta Kano.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Jama'a na ta kansu, ana ta harbe-harbe a kusa da' ofishin INEC a jihar Taraba

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani abokin mamacin, wanda ya bukaci a sakaya sunan shi, ya ce ba zai iya bayyana komai dangane da lamarin ba har sai samu nutsuwa daga firgicin da ya ke ciki.

An ruwaito cewa kafin faruwar lamarin a ranar, marigayin ya kawo abinci ga wakilan jam'iyyun APC da NNPP a akwatinsa.

Makusanta sun ce ba zai yi wu ace an kama shi da yunkurin satar akwatun kuri'a ba.

Nakuzama ya mutu ya bar mata biyu da yaya shida.

Wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi wani wanda abin ya faru a gabansa, wanda ya ce sunansa Muhammad Hassan Getso, mazaunin Damunawa a Kano don samun karin bayani inda ya ce:

"Rikici ne ya balle a akwatin zaben bayan an samu rashin fahimta tsakanin wakilan jam'iyyu, jama'a ma suka hargitse, a kokarin daidaita al'amura jami'an tsaro suka yi harbi wadda har ya jikkata wasu mata biyu wadanda ke asibiti a halin yanzu suna karbar magani.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bidiyon yadda aka ga kwamishinan jihar Arewa yana raba kudi gabanin zabe

"Shi kuma sai ya yi wajen akwatin zaben da nufin ya kare ta kada a lalata, sai jami'an soja suka yi harbe shi bisa tunanin satar akwatin ya je."

Martanin jami'an tsaro kan lamarin

Yunkurin jin ta bakin sojoji dangane da lamarin ya ci tura har zuwa lokacin kammala wannan rahoton yayin da mai magana da yawun yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba shi da masaniya akan batun amma zai yi bincike.

Tun da farko dai yan sanda sun kama mutane uku, da su ka hada da Bashir Nasiru Aliko Koki, manajan daraktan Kano Line, da yunkurin satar akwatun zabe a Gwammaja da ke karamar hukumar Dala a jihar.

Daily Trust ya ruwaito cewa akwai rahotannin lalata kuri'a a mazabu da dama a karamar hukumar Rimin Gado a jihar.

Bidiyon Kwamishinan Bauchi yana rabon kudi gabanin zaben gwamna

A wani rahoton kuma, kun ji cewa wani bidiyo ya yadu a dandalin sada zumunta inda aka gano wani da aka ce kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi, Adamu Manu Soro ne yana rabon kudi gabanin zabe.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Sanda Sun Ceto Jami’an INEC 19 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Safiyar Yau Asabar

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel