2027: APC Ta Bazama Ketare Neman Kuri’un Mutane saboda Zaben Tinubu
- Jam’iyyar APC reshen Amurka ta fara ƙara ƙaimi wajen tattara ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje
- Shugabannin reshen jam'iyyar sun yaba da ƙoƙarin haɗa kan magoya bayan APC a ƙasashen waje, suna cewa hakan zai ƙarfafa jam’iyyar
- APC-USA ta buƙaci ‘yan Najeriya mazauna ƙetare su ƙara bayar da gudunmawa da sababbin dabaru domin tallafa wa Renewed Hope
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Jam’iyyar APC reshen Amurka ta ƙara ƙaimi wajen kira ga haɗin kan ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje yayin zaben 2027 ke matsowa.
Jam'iyyar APC ta bukaci goyon bayansu inda ta ce hakan zai kasance muhimmi ga nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da ya fitar wanda Punch ta samu, shugaban APC-USA, Taiwo Balofin, ya yaba wa shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda.
An fara nemawa Tinubu goyon baya a ketare
Kungiyar ta kuma yaba da ƙoƙarin shugabannin jam’iyyar da mambobin kungiyar Renewed Hope Ambassadors wajen haɗa kan magoya bayan APC a ƙasashen waje.
Ya kuma yaba wa gwamnan Hope Uzodimma, wanda shi ne babban daraktan Renewed Hope Ambassadors, saboda ƙoƙarinsa na ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobin jam’iyyar.
Balofin ya ce ƙarfafa sadarwa kan gyare-gyaren gwamnati da nasarorin da aka samu, tare da wayar da kan ‘yan Najeriya mazauna ƙetare, zai ƙara wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu goyon baya.
Ya ce:
“Kiran haɗin kai da ingantacciyar sadarwa game da nasarorin gwamnati abu ne mai kyau wanda zai ƙarfafa goyon bayan gwamnatin Tinubu.”

Source: Facebook
Alwashin da yan APC mazauna ketare suka yi
Shugaban APC-USA ya kuma yaba wa shugabar hukumar yan Najeriya da ke ketare, Abike Dabiri-Erewa, saboda ƙoƙarinta na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.
Balofin ya tabbatar da cewa shugabanni da mambobin APC a ƙasashen waje za su ci gaba da aiki tare domin inganta martabar jam’iyyar da kuma bayyana nasarorin gwamnatin Tinubu a duniya.
Sai dai ya buƙaci shugabannin jam’iyyar su rika bai wa mambobin APC na ƙasashen waje goyon baya da amsoshi cikin gaggawa idan buƙata ta taso, cewar Daily Post.
A shekarun baya-bayan nan, ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje sun zama muhimmiyar ƙungiya ga jam’iyyun siyasa ta fuskar yaɗa manufofi, tara magoya baya da hulɗar ƙasa da ƙasa.
Ko da yake har yanzu ba a fara zaɓen ‘yan Najeriya mazauna ƙetare ba, jam’iyyun siyasa na ci gaba da neman goyon bayansu saboda tasirin da suke da shi wajen tsara ra’ayin jama’a da yaɗa manufofinsu a duniya.
Murabus: APC ta yi yan majalisa martani
An ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta soki jam’iyyun adawa bisa goyon bayan kiran Bola Tinubu ya sauka daga mulki saboda matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya.
Wasu 'yan majalisar wakilai sun bukaci shugaba Tinubu ya dakatar da harkokin 2027 tare da ƙaddamar da shiri na wata shida kan tsaro da tattalin arziki.
Sai dai jam’iyyar APC ta jaddada cewa gwamnatin Tinubu na ɗaukar matakan da suka dace domin magance ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a yanzu.
Asali: Legit.ng

