Zaben 2023: An Nemi Masu Jefa Kuri’a Su Rantse Kafin Su Karbi Taliya da Tufafi a Jihar Neja

Zaben 2023: An Nemi Masu Jefa Kuri’a Su Rantse Kafin Su Karbi Taliya da Tufafi a Jihar Neja

  • A jihar Neja, an tono yadda ‘yan siyasa ke amfani da kayan abinci da tufafi wajen sayen kuri’u a zaben bana na 2023
  • Wannan lamari dai ya ba da mamaki, domin wata mata ta bayyana yadda ake ba da yadin atamfa daya ga mutanen jihar
  • Ba sabon abu bane a Najeriya a yi sayen kuri’u a duk lokacin da zabe ya tashi, musamman a irin wannan yanayin

Jihar Neja - Wasu masu kada kuri’u a jihar Neja sun ce, wasu ‘yan siyasa sun nemi su nuna katunan zabensu sannan su rantse za su zabi ‘yan takarar da suke so kafin ba su kayan amfanin gida.

Daga cikin kayayyakin da aka ce za a basu akwai bokitai, taliya, kayan sakawa da Maggi, kuma hakan ba sabon abu bane a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Masu sayen kuri'u sun taru, sun lakadawa jami'an EFCC duka a jihar a Arewa

Daily Trust ta tattaro cewa, ‘yan siyasa a Najeriya na amfani da kayayyakin aikin gida, sutura da kayan abinci wajen sayen kuri’un al’ummar Minna a Neja da sauran garuruwa.

Yadda 'yan siyasa ke sayen kuri'u a Neja
Jihar Neja da ke Arewacin Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wasu masu kada kuri’un sun shaidawa jaridar cewa, an nemi su nuna katin zabe sannan su rantse da Allah za su zabi wasu ‘yan takara domin samun kayan duniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda ake rabon kayan abinci da tufafi ga mata

A yankin Tunga na Minna a jihar, wata daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan rabon kayan abinci, Mrs Jamila Muhammad ta ce, ta samu takiyar girkawa.

A cewarta:

“Yadi daya ake ba mutum daya na kayan sakawa. Meye mutum zai yi da yadi daya na kaya? Ba zai isa ko da karamin yaro bane.
“Na karbi taliya, amma duk da haka sai da muka yi fada da mutane saboda mun yi yawa. Idan kaga yadda mata ke kokuwa kan taliya, abin da ban mamaki.”

Kara karanta wannan

'Yunwa A Ƙasa': Masu Kaɗa Ƙuri'a Sun Ƙi Karɓar Tiransifa, Sun Buƙaci Abinci A Babban Jihar Arewa

Wasu ba sa karbar kudin 'yan siyasa

Wata mata ta daban a Dutsen Kura Hausa, Baba Usman ta shaidawa jaridar cewa, wasu ‘yan siyasan suna raba shinkafa da tufafi, inda suka yi alkawarin yi musu alheri idan suka lashe zabe.

A Bida, wani mai kada kuri’an da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, akwai mutane da yawa da suka ki karbar irin wannan kayan sayen kuri’u daga ‘yan siyasa.

A wasu garuruwan, an saye kuri’un jama’a ne da kayan abinci ba da kudi ba saboda halin da ake ciki na kuncin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel