'Yan Daba Masu Sayen Kuri’u Sun Farmaki Jami’an Hukumar EFCC a Jihar Kaduna

'Yan Daba Masu Sayen Kuri’u Sun Farmaki Jami’an Hukumar EFCC a Jihar Kaduna

  • Rahoto ya bayyana yadda 'yan jihar Kaduna suka farmaki jami'an hukumar EFCC mai yaki da rashawa a kasar nan
  • Wannan lamarin ya faru ne a rumfunan zabe a daidai lokacin da wasu ke shirin sayen kuri'un talakawa a jihar
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha a fadin kasar nan

Jihar Kaduna - An farmaki jami’an hukumar EFCC da ke aikin sanya ido kan zabe a jihar Kaduna a Unguwan Rimi da ke birnin a lokacin da suke kokarin kama wani bata-gari mai sayen kuri’u

Wata sanarwa da jaridar Leadership tace ta samo dauke da sa hannun mai magana da yawun EFCC, Mr. Wilson Uwujare ta ce, jami’an na ta kiwon wani Kabiru Musa ne da aka ce yana sayen kuri’u bayan yaduwar wani bidiyo.

Kara karanta wannan

Ku rantse za ku zabe mu: Yadda 'yan siyasa ke yarjejeniya da jama'a kafin siyan kuri'unsu da taliya a Neja

An ruwaito cewa, an ga Musa a wani bidiyo yana kokarin yaudarar masu kada kuri’u ta hanyar nuna musu zai sayi kuri’unsu tae da yi musu tiransfa na kudin zuwa asusun banki.

Yadda aka farmaki jami'an EFCC a Kaduna
Jami'an hukumar EFCC mai yaki da rashawa | Hoto: vanguardngr.com

Yadda 'yan daba suka farmaki jami'an EFCC

Sai dai, bayan kama shi, hukumar ta ce ya ui kururuwa, lamarin da yasa abokan cin mushensa suka taso tare da farmakar jami’an da ke bakin aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Wilson, ‘yan daban sun farmaki jami’an EFCC da makamai, har ta kai aka jikkata wasu daga cikinsu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Duk da haka, ya ce jami’an basu hakura, sai da suka tabbatar da kama wanda ake zargin don tabbatar da gaskiyar abin da ake zargi, Channels Tv ta ruwaito.

Kakakin na EFCC ya yi kira ga jama'a da su guji farmakar jami'an da ke aiki don tabbatar da kariyar al'umma daga fadawa hadari mai zurfi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gobara Ta Sake Tashi A Wata Babban Kasuwar Borno, Hotuna Sun Fito

Sai mata sun rantse kafin a basu taliya a Neja

A wani labarin, ana kulla yarjejeniya tsakanin masu akda kuri'u da 'yan siyasa a wurin zaben gwamna da aka yi a jihar Neja.

Rahoto ya bayyana yadda jama'a ke rantsewa kafin a basu ledar taliya, bokiti ko kayan abinci a jihar da ke Arewa.

An yi azababben sayen kuri'u a wannan zaben, lamari ya ba da mamaki a yankuna daban-daban na kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel