Jam'iyyar PDP Ta Lallasa APC a Gidan Gwamnatin Malam El-Rufai

Jam'iyyar PDP Ta Lallasa APC a Gidan Gwamnatin Malam El-Rufai

  • Jam'iyyar APC mai mulkin Kaduna ta kwashi kashinta a hannu a sakamakon zaben rumfuna 2 na gidan gwamnatin El-Rufai
  • Isa Ashiru Kudan ya samu nasara a kan babban abokin adawarsa na APC, Uba Sani da rumfunan zaɓe PU 013 da PU 014
  • Kawo yanzu dai sakamakon zaben gwamnonin da aka gudana a jihohun Najeriya na cu gaɓa da fitowa daga rumfunan zabe

Kaduna - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta sha ƙasa a rumfunan zaɓe biyu da ke cikin gidan gwamnatin jihar Kaduna (Sir Kashim Ibrahim House).

Ɗan takarar gwamnan Kaduna a inuwar PDP, Isa Ashiru Kudan, ya samu nasara a zaben akwatun PU 014 da ƙuri'u 77 yayin da Sanata Uba Sani na jam'iyar APC ya samu kuri'u 40.

Gwamna El-Rufai.
Jam'iyyar PDP Ta Lallasa APC a Gidan Gwamnatin Malam El-Rufai Hoto: GovernorKaduna
Asali: UGC

Babban malamin zabe a rumfar, PO Mohammed Baso, ya sanar da cewa Labour Party ta tashi a tutar babu, NNPP ta sami kuri'a 1, PRP ta tashi da guda 1. Ya ce an samu lalatattun kuri'u 7.

A rumfa mai lamba 013, shi ma a cikin gidan gwamnatin Kaduna, PDP ta samu kuri'u 69, yayin da babbar abokiyar fafatawarta APC ta tashi da kuri'u 64, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A halin yanzu, Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sakamakon zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokokin jihohi da aka gudanar yau Asabar sun fara fitowa daga rumfunan zaɓe.

Zaben yau 18 ga watan Maris, 2023 ya gudana ne a jihohin Najeriya 28, yayin da sauran guda 8 kum aka fafata zaben 'yan majlsar jihohi, kamar yadda Punch ta rahoto.

Wannan karon dai an tattato cewa na'urar BVAS tana tura sakamako kai tsaye ga Fotal ɗin INEC sabanin matsalar da aka samu a zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

INEC ta shawo kan matsalar tura sakamako da BVAS

A wani labarin kuma INEC Ta Fara Dora Sakamakon Zaben Gwamnoni da yan majalisar jihohi da Na'urar BVAS

Sabanin abinda ya faru a zaben shugaban kasa da ya gabata. INEC ta fara ɗora sakamakon zaben yau Asabar da na'urar BVAS An sha cece-kuce a zaben shugaban kasa kan rashin ɗora sakamakon da na'urar, lamarin da ya sa wasu ke tantamar sahihancin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel