Yadda Aka Dauki Bidiyon Kwamishinan Bauchi Yana Raba Kudi Gabanin Zaben Gwamna

Yadda Aka Dauki Bidiyon Kwamishinan Bauchi Yana Raba Kudi Gabanin Zaben Gwamna

  • Wani bidiyo ya nuna lokacin da wani kwamishinan jihar Bauchi ke ba da kudi ga wasu mutane a jajiberin zaben gwamnoni
  • Bidiyon da muka ya nuna cewa, alamu sun bayyana yana kokarin ba da kudin ne don jan hankalin masu kada kuri'u
  • Ba sabon abu bane a Najeriya 'yan siyasa su saye kuri'u daga hannun talakawan gari a duk sadda zabe ya tashi

Jihar Bauchi - Wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta ya nuna lokacin da kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi, Adamu Manu Soro na rabon kudi gabanin zaben gwamna.

A bidiyon, an ga yana zagaye da 'yan sandan da ke ba shi kariya a lokacin da yake rabon kudin a ranar Juma'a; jajiberin zaben gwamnoni da 'yan majalisar wakilai.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sha bayyana matsayarta na yakar masu siyan kuri'u a zaben bana.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rikici Ya Kara Tsananta a Kano, An Wargaza Akwatunan Zabe Sama da 10

Yadda kwamishinan Bauchi ya yi siyan kuri'u
Jihar Bauchi, daya daga jihohin Arewa maso Gabas | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hakazalika, an ce an tura jami'an tsaro a yankuna daban-daban don kama masu siyan kuri'u a yankunan kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zuwa yanzu dai, ana ci gaba da samun rahotannin yadda ake ganin masu siyan kuri'u a kasar.

Ana raba kudi ga mata, da matasa

A bidiyon da muka gani, akwai tarin mata da ke layi suna karbar kudin daga hannun kwamishinan.

Daga cikin matan, akwai wadanda ke dauke da kananan yara a lokacin da kwamishinan ke tsaye yana kirga kudade a gefe.

Wata murya da ke cikin bidiyon na cewa, duk matar da aka ba ta kudi ta tabbata ta zabi lema; wato jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.

Kalli bidiyon:

Ba lallai gwamnan Bauchi ya ci zabe ba

A wani labarin, rahoto ya bayyana jerin wasu gwamnoni biyar masu ci da ake tunanin ba lallai su ci zaben da aka yi a bana ba na gwamnoni.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mataimakin Gwamnan Jam'iyyar APC da Ya Sauka Ya Mutu

Daga cikinsu, akwai gwamnan jihar ta Bauchi, Bala Muhammad duba da wasu dalilai da kuma karfi da tasirin dan takarar jam'iyyar APC a jihar da ke Arewa maso Gabas.

A yau dai an yi zabe, ana ci gaba da kirga kuri'u domin sanin wanda ya lashe zaben gwamna da na 'yan majalisun jiha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel