'Yunwa A Ƙasa': Masu Kaɗa Ƙuri'a Sun Ƙi Karɓar Tiransifa, Sun Buƙaci Abinci A Babban Jihar Arewa

'Yunwa A Ƙasa': Masu Kaɗa Ƙuri'a Sun Ƙi Karɓar Tiransifa, Sun Buƙaci Abinci A Babban Jihar Arewa

  • Tsananin yunwa da ake fama da ita a kasa ya janyo masu kada kuri'a sun bukaci a ba su abinci kafin su yadda su kada kuri'a a sassan Jihar Niger
  • Masu kada kuri'a sun ce babu wata hanya da su ke morar yan siyasa, saboda haka dole su karbi wani abu a wajen yan siyasa duk da suna sane da hakan ba daidai bane
  • An ruwaito cewa ana raba kudi, atamfa, da kuma alkawarin taransifa sai dai mutane sun ki amincewa da alkawarin taransifa saboda an ci amanar su a zaben baya

Niger - Masu kada kuri'a da dama a Garam, wani gari a karamar hukumar Tafa da ke Jihar Niger, sun ki amincewa da alkawarin taransifa da wakilan jam'iyyu ke yi mu su tare da neman a ba su abinci a matsayin sharadi kafin su kada kuri'a a zaben ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Sanda Sun Ceto Jami’an INEC 19 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Safiyar Yau Asabar

Wasu daga cikin masu zaben sun ce sun dauki wannan matakin dalilin abin da ya faru a zaben shugaban kasa na 25 da watan Fabrairu, na kin cika mu su alkawarin da aka yi mu su, rahoton Daily Trust.

Abinci
Masu Kaɗa Ƙuri'a Sun Ƙi Karɓar Tiransifa, Sun Buƙaci Abinci A Neja. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Wakilin majiyarmu ya lura da yadda ake raba wa masu zabe kudi, wasu ta taransifa, atamfofi da kuma kudi hannu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalilin da yasa muka karba kaya daga hannun yan siyasa, Mai kada kuri'a

Daya daga cikin masu zaben, wacce ta bayyana sunanta a matsayin Angela, ta ce sun sani cewa abin da suka yi ya saba da kundin tsarin mulki da kuma tarbiya karbar wani abu daga hannun yan siyasa don zabar su amma ya zama kamar ita kadai ce ta morar mutanen da ta kira masu son kai.

Kara karanta wannan

Mota Dauke Da Yara Yan Makarantar Firamari Ta Yi Kundunbala A Legas

Ta ce:

'Kalli titunanmu, a lalace. Da sun samu abin da su ke so ba za mu kara ganin su ba. To a bari mu samu abin da za mu samu yanzu.''

Wani mai zabe a akwatu ta 001 ta Kofar Sarki ta ce duk jam'iyyu su na siyan kuri'a a yankin.

Ta ce wasu sun bada atamfa, wasu kudi, wasu kuma sun yi alkawarin taransifa.

''Wanda su ka yi alkawarin taransifa za su yi nadama yau saboda abin da su ka yi lokacin zaben shugaban kasa. Sun yi alkawari amma har yanzu, ba wanda su ka biya. To da su ka zo da wannan dabarar yau, ma su zabe ihu su ka yi musu,' a cewarta.

Bidiyon Kwamishinan Bauchi yana rabon kudi gabanin zaben gwamna

A wani rahoton kuma, kun ji cewa wani bidiyo ya bazu a dandalin sada zumunta inda aka gano wani da aka ce kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi, Adamu Manu Soro ne yana rabon kudi gabanin zabe.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Rundunar Yan Sanda Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al’ummar Jihar Kano Ana Gab Da Zabe

Ana iya ganin wasu jami'an yan sanda biyu a kusa da shi yayin da mutane ke kan layi suna karbar sabbin kudin sannan ana musu tunin kada su ci amana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel