An Bindige Shugaban Kamfen Jam’iyyar APC, Ya Mutu Yana Kokarin Hana Ayi Murdiya

An Bindige Shugaban Kamfen Jam’iyyar APC, Ya Mutu Yana Kokarin Hana Ayi Murdiya

  • APC ta rasa Shugaban yakin neman zaben Gwamna a karamar hukumar Ahoada yamma a Ribas
  • Ana tunanin Chisom Lennard ya rasu ne yana kokarin hana ‘yan daba su sace kayan zabe a Ibagwa
  • Lennard jagora ne na jam’iyyar APC, yana cikin masu tallata Tony Cole ya zama Gwamna a Jihar

Rivers - Shugaban yakin neman zaben jam’uiyyar APC a karamar hukumar Ahoada yamma a jihar Ribas, ya mutu bayan ‘yan bindiga sun harbe shi.

The Guardian ta kawo rahoto a safiyar Lahadi cewa an kashe Chisom Lennard wanda shi ne shugaban APC na mazabarsa ya bakunci barzahu.

An harbe Chisom Lennard ne a yayin da yake kokarin hana wasu miyagu da suka yi shigar ‘yan sanda, su na yunkurin satar kayan zabe a Ibagwa.

Kakakin kwamitin takarar Rivers APC 2023, Sogbeye Eli ya shaidawa jaridar cewa wadannan bata-gari sun bude masa wuta, nan take ya hallaka.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba na yiwa jama'a barazar ko su zabi APC ko su su dauki wani mataki a wata jiha

Maganar Sogbeye Eli

"Eh, kwarai, an kashe shugaban kwamitin neman takararmu na karamar hukumar Ahoada yamma a jihar Ribas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An harbi Chisom ne a lokacin da yake kokarin hana wasu miyagu masu dauke da kayan ‘yan sanda satar kayan zabe.
Sun harbe shi, kuma nan take ya mutu."

- Sogbeye Eli

'Yan sanda
'Yan sanda a bakin aiki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

APC tayi rashi a Ahoda

Marigayin yana cikin wadanda ke kan gaba wajen tallata Tonye Cole na jam’iyyar APC a Ahoda, baya ga haka yana digirinsa na PhD a jami’ar jihar Ribas.

Punch ta ce sai da aka dauke ‘dan siyasar aka yi gaba da shi, sannan sai aka ji labarin an yi amfani da bindiga an harbe shi, hakan ya yi sanadiyyar ajalinsa.

Darlington Nwauju wanda shi ne Sakataren yada labaran APC na Ribas ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da Marigayin ne, suka tafi wani wuri da shi.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Daba Sun Halaka Jigon PDP Kuma Kansila, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sha da Kyar

“Babu wanda ya san inda suka kai shi. Da yammacin Asabar ne aka tsinci gawarsa.”

- Darlington Nwauju

Babatun Rotimi Amaechi

An ji labari Rotimi Amaechi wanda ya yi Gwamna na shekaru takwas a Ribas ya ce Shugaban hukumar INEC yana da alaka da Gwamna Nyesom Wike.

Amaechi ya ce ‘Yan sanda su na taimakawa PDP wajen cafke ‘yan APC da SDP, ‘dan siyasar ya ce da INEC suke takarar Gwamna da majalisu ba PDP ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel