Kwamishinan Hukumar INEC Na Jihar Legas Ya Dage Zaben Yankin VGC Zuwa Gobe Lahadi

Kwamishinan Hukumar INEC Na Jihar Legas Ya Dage Zaben Yankin VGC Zuwa Gobe Lahadi

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta dage zaben gwamna a wasu yankunan jihar Legas saboda wasu dalilai
  • Jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya na daya daga wadanda hankalin jama'a ya karkata a kansu a zaben bana
  • Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a bayyana matsalar da ka samu ba da ta kai ga dage zaben na bana

Jihar Legas - Kwamishinan hukumar zabe ta INEC a jihar Legas, Mr. Olusegun Agbaje ya bayyana dage zaben gwamnoni da ‘yan majalisu a yankin VGC a jihar Legas.

A cewar kwamishinan, za a yi zaben ne a gobe Lahadi 19 ga watan Maris farawa daga karfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na yamma, Tribune Online ta ruwaito.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani daga majiyarmu na dalilin da yasa aka dage zaben na yau Asabar 18 ga wata.

An dage zabe a wani yankin Legas
Gwamnan Legas Sanwo Olu | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Bayanin kwamishinan INEC lokacin da ya dage zaben

Da yake magana yayin daga zaben, Daily Trust ta ruwaito kwamishinan na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna da rumfunan zabe masu adadin masu kada kuri'u 6,024 wanda daga cikinsu mutum 5,624 suna katunan PVC.
"Bayan duba cikin tsanaki da kuma umarni daga matakin hedkwata a kasa za mu sake yin zaben gobe (Lahadi) da safe 8:30.
"Da safiyar gobe (Lahadi) za mu sake taruwa a nan."

Ba wannan ne karon farko da ake dage zaben gwamna ko na 'yan majalisa ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa a lokuta daban-daban.

Ana kyautata zaton ba wata matsala mai girma bace ta kai dage wannan zabe na yankin Victoria a jihar ta Legas.

Gwamnan Legas zai iya cin taliyar karshe

A wani rahotonmu na baya, kun ji yadda aka bayyana hasashen sakamakon zaben gwamnoni da ke tafiya a Najeriya a wannan shekarar ta 2023 da ake ciki.

Ana hasashen cewa, gwamna Sanwo Olu na jihar Legas ba lallai ya kai labari ba a zaben, duba da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi, inda Peter Obi ya lashe kuri'un jihar Legas.

Wannan na da nasaba da yadda Inyamurai suka mamaye Legas, lamarin da ya sa Tinubu bai ci jiharsa ba a zaben na bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel