Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP A Cikin Gidan Gwamnati Na Ortom

Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP A Cikin Gidan Gwamnati Na Ortom

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta kwashi kashinta a hannu a sakamakon zaben akwatuna biyu na gidan gwamnatin Samuel Ortom
  • Rabaran Fada Hyacinth Alia na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya samu jimillar kuri'u 166 a akwatunan biyu na gidan gwamnati yayin da abokin karawarsa ya samu 43
  • Kawo yanzu dai sakamakon zabukan suna cigaba da fitowa daga akwatinan zabe daga sassan na jihar Benue

Benue - Dan takarar Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Rabaran Fada Hyacinth Alia, ya lashe akwatunan zabe biyu da ke cikin gidan gwamnatin jihar Benue da ke Makurdi, Daily Trust ta rahoto.

Alia, dan takarar na APC ya samu kuri'u 130 inda ya kada abokin karawarsa na PDP, Injiniya Titus Uba, wanda ya samu kuri'u 43 a akwatin zabe mai lamba 001 na Arts Theatre.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Lallasa APC, Ta Lashe Rumfuna 2 a Gidan Gwamnatin Kaduna

Gwamna Ortom
Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP A Cikin Gidan Gwamnati Na Ortom. Hoto: The Nation
Asali: UGC

A kuma akwatin zabe na Protocol mai lamba 022, jam'iyyar APC ta samu kuri'u 36 yayin da PDP ta samu kuri'u 0.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Samuel Ortom na cikin gwamnoni bakwai da suka sha kaye a yunkurinsu na zuwa majalisar dattawa.

A matsayinsa na mamba na tawagar gwamnonin G5 karkashin jagoranci Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, Samuel Ortom yana ta faman kokarin yadda zai kawo yankinsa.

Yunwa ta saka masu zabe sun ce a rika basu abinci a madadin tiransifa

A wani rahoto daban kun ji cewa wasu mutane a wani gari mai suna Garam da ke karkashin karamar hukumar Tafa a jihar Neja sun ki amincewa da alkawarin tura musu kudi ta hanyar tiransifa daga wakilan jam'iyyu.

Masu kada kuri'un sun ce idan ba sun ga kudi ko abinci a kasa ba, ba za su jefa kuri'a ga jam'iyyun da wakilan ke so ba, suna mai cewa a yayin zabukan shugaban kasa an yaudare su an ce za su ga tiransifa amma ba su ga komai ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mataimakin Gwamnan Jam'iyyar APC da Ya Sauka Ya Mutu

Wasu cikin mutanen sun bayyana cewa sun san karbar toshi daga hannun wakilan jam'iyyu ya saba dokar zabe a kasa amma sunce wannan ce hanya guda da za su iya morar wani abu daga yan siyasan shi yasa suka dage.

Asali: Legit.ng

Online view pixel