Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Katsina da Taraba

Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Katsina da Taraba

Allah ya kawo mu.

A yau Asabar 18 ga watan Maris, 2023 za'a gudanar da zaben gwamnoni da yan majalisar jihohi bayan tsaikon da aka samu har INEC ta ƙara mako ɗaya.

Legit.Hausa ta shirya tsaf don kawo muku yadda zaben ke gudana a Katsinan dikko da kuma Taraba, ku kasance tare da ni Ahmad Yusuf a wannan shafin.

Katsina

Tsohon shugaban SMEDAN, Dakta Dikko Raɗɗa, na jam'iyyar APC ke kokarim gaje Masari amma Sanata Yakubu Lado na PDP na fafutukar raba canza canji.

Taraba

Idan muka leƙa jihar Taraba kuma, Emmanuel Bwacha, ne ke neman zama gwamna a inuwar APC yayin da tsohon soja, Kanal Kefas Agbu, ke fatan gaje gwamna mai ci a inuwar PDP.

Ɗan takarar gwamnan APC, Dikko Radda ya kaɗa kuri'a

Mai neman zama gwamnan jihar Katsina a inuwar jam'iyar APC, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa, ya kaɗa kuri'arsa.

Dikko Umaru Raɗda.
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Katsina da Taraba
Asali: Facebook

Dan takarar gwamnan PDP ya kaɗa kuri'a

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina karkashin inuwar PDP, Sanata Garba Yakubu Lado Ɗanmarke, ya kaɗa kuri'arsa a mazaɓarsa da ke Ɗanmarke, karamar hukumar Kankara.

Yakubu Lado Danmarke.
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Katsina da Taraba
Asali: Facebook

Matar Radda Ta Jefa Kuri'a

Hajiya Fatima Dikko Ummaru Raɗɗa, matar ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a inuwar jam'iyyar APC mai mulki ta ƙaɗa kuri'a.

Hajiya Fatima Dikko Radda.
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Katsina da Taraba
Asali: Facebook

Tsohon gwamna, Barista Shema ya kaɗa kuri'a

Tsohon gwamnan jihar Katsina na tsawon zango biyu, Barista Ibrahim Shehu Shema, ya kaɗa kuri'arsa a mzabarsa da ke yankin ƙaramar hukumar Dutsin-ma jihar Katsina.

Ibrahim Shema
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Katsina da Taraba
Asali: Facebook

Rumafar zabe mai mutum 13 kacal a Dabai

Malaman zaɓe na wucin gadi na zaune suna jiran mutane 13 kacal da suka yi rijistar zaɓe a PU 022 da ke gundumar Dabai, ƙaramar hukumar Ɗanja.

Yayin da wakilin Legit.ng Hausa ya ziyarci rumfar zaben, ya samu bayanin cewa mutane 7 sun samu damar kaɗa kuri'a, saura mutum 6 ake jira.

Zaben Katsina.
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Katsina da Taraba
Asali: Original

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaɗa kuri'a

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kaɗa kuri'arsa a zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki da ke gudana yau Asabar 18 ga watan Maris, 2023 a Katsina.

Buhari ya jefa kuri'rasa a mazabarsa da ke Daura kamar yadda, Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani ya wallafa.

Zabe ya kankama a Dabai Ward, Danja LGA

Zabe ya kankama a PU OO1 da ke makarantar Model Firamare Dabai, ƙaramar hukimar Ɗanja a jihar Katsina.

Wakilimmu ya ziyarcu wurin kuma ya tarad da mutane a kan layi suna jira a tantance su kana su kaɗa kuri'unsu ga yan takarar da suka kwanta masu a rai.

Zaben Katsina
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Katsina da Taraba
Asali: Original

An fara kaɗa kuri'a a Mashi LG

Tuni Malaman zaɓe suka gama shiri kuma har mutane sun fara kaɗa kuri'unsu a rumfar zabe ta 005 da ke makarantar Firamarea Gamzo, ƙaramar hukumar Mashi, jihar Katsina.

Zabe ya kankama a karamar hukumar Mashi.
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Katsina da Taraba
Asali: Facebook

Online view pixel