Siyasar Najeriya
Shugabannin kananan hukumomi 23 da gwamnatin jihar Benue ta dakatar sun nunawa Gwamna Hyacinth Alia yatsa. Sun sha alwashi cewa ba zasu sauka daga kujerunsu ba.
Wani matashi dan Najeriya ya bayyana irin matsalar da ya samu daga yadda aka ce za a sama masa aiki daga kamfani idan ya kammala karatu, amma abu ya gagara.
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Reno Omokri ya bayyana cewa karya ne ace shugaban kasa Bola Tinubu bai halarci jami'ar jihar Chicago da ke kasar Amurka ba.
Tsohon kwamishina a jihar Ribas, Augustine Wokocha, ya ce ba ya adawa da yunkurin sauya sheƙar Nyesom Wike daga PDP zuwa APC amma ba zai yuwu ya zama jagora ba.
Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya sake karban dandazon masu sauya sheka daga PDP zuwa APC maulki, ya ce duk an zama ɗaya babu wanda zai nuna musu banbanci.
Gwamnan jihar Ebonyi mai ci, Francis Nwifuru, ya umarci tsoffin kwamishinoni, waɗanda suka yi aiki da tsohon gwamna su bar gidajen gwamnati cikin mako biyu.
Jam'iyyar PDP reshen Benuwai ta caccaki gwamnatin PDP karkashin mulkin gwamna Hyacinth Alia dangane da matakin da ya ɗauka kan ciyamomin kananan hukumomi 23.
Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato, ya nada sakataren gwamnati, shugaban ma'aikata da masu ba da shawara da mataimaka na musamman a gwamnatinsa ranar Laraba.
Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato ya sallami Sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 23 daga bakin aiki yayin da ake ci gaba da sauraron karar zaɓe a Kotu.
Siyasar Najeriya
Samu kari