Fastoci Sun Ayyana Cikakken Goyon Baya Ga Gwamna Mai Jiran Gado a Kaduna

Fastoci Sun Ayyana Cikakken Goyon Baya Ga Gwamna Mai Jiran Gado a Kaduna

  • Ƙungiyar Limaman Coci ta kaiwa zababben gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ziyara ta musamman bayan cin zaɓe
  • Fastocin sun faɗa wa Uba Sani cewa suna tare da gwamnatinsa kuma har wani suna aka laƙaba musu 'Fastocin APC'
  • Sun ce ko bacci ba su iya yi lokacin zabe saboda barazanar da ake musu amma suka tsaya kai da fata

Kaduna - Ƙungiyar Malaman Coci-Coci sun ziyarci zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, kuma sun ayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin APC ta gaba.

Fasto-Fasto din sun bayyana cewa duk da ana kiransu da "Limaman Coci na APC," suna karkashin ƙungiyar Progressive Pastors reshen jihar Kaduna, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Malam Uba Sani.
Gwamnan Kaduna mai jiran Gado, Sanata Uba Sani Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Limaman Cocin karkashin jagorancin Rabaran Ayokunle Adebayo, sun ce sun damu matuƙa da habaka da ci gaban da ake gani a Kaduna, saboda haka suna fatan shiga gwamnatin Uba Sani.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta Kunshe Biliyoyin Kudi Wajen Saida Fam Ga Masu Sha’awar Takara

Wasu daga cikin Fastocin da suka yi zargin CAN ta banzatar da su kuma an yi wa manyansu barazana lokacin zaɓe dun haɗa da, Rabaran.Emmanuel Ayokunke Adebayo, Fasto Madugu, Elder Godson Eyitayo, da Fasto Ruth Waziri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran sun ƙunshi Misis Jumnai Adamu, Wisdom Alpabio, Emmanuel John, Fasto Samuel Aska, Rabaran Seth Yahaya Bako, Rabaran Boru da kuma Rabaran Elisha Bulus.

Ko'odinetan ƙungiyar Progressive Pastors ta jihar Kaduna, Rabaran Adebayo, ya ce da yawan mutane na kiransu Fastocin APC amma hakan bai dame su ba ko kaɗan.

"Tunda aka fara zaɓe bana iya bacci sabida barazanar kawo hari," Shugaban Kiristocin ya faɗa wa Malam Uba Sani.

Ya yi zargin cewa akwai wuraren da aka yi magudi sosai lokacin zaɓe amma suka tsaya kai da fata. Ya ce, "Duk da CAN ta jingine mu, zamu goyi bayanka nan da shekaru 4 ko sama da haka."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikici Ya Tsananta, Gwamna Wike Ya Maida Martani Mai Zafi Kan Dakatar da Shugaban PDP

Sanata Uba Sani da fuskarsa ta nuna yana cikin farin ciki ya ɗauki Hotuna da Fastocin kuma ya tabbatar musu da cewa Kaduna zata ƙara dunƙulewa a mulkinsa.

Ayu Bai Nemi Zaman Lafiya Ba Idan Ya Yi Fatali da Umarnin Kotu, Bode George

A wani labarin kuma Shugaban PDP na ƙasa ya shiga tsaka mai wuya bayan Kotu ta dakatar da shi

Babbar jam'iyyar adawa na fama da rigingimun cikin gida tun kafin zaɓe, bayan gama zabe kuma lamarin ya ɗauki sabon salo musamman a yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel