Hukumar Zabe Ta INEC Ta Ce Za a Kammala Sauran Zabukan Najeriya da Suka Rage a Ranar 15 Ga Afrilu

Hukumar Zabe Ta INEC Ta Ce Za a Kammala Sauran Zabukan Najeriya da Suka Rage a Ranar 15 Ga Afrilu

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanya ranar karasa zabukan da aka yi ba a kammala ba a Najeriya
  • A ranar 15 ga watan Afrilu ne za a karasa zabukan, kamar yadda INEC ta bayyana a yau Litinin 27 ga watan Maris
  • An samo tsaiko a wasu bangarori daban-daban an Najeriya, an soke sakamako, an kuam dage sanar da sakamakon zabe

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanya ranar da za ta kammala zabukan da suka rage ba a yi su ba a Najeriya na bana.

Hukumar ta ce, za a kammala sauran zabukan gwamna, na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi ne a ranar 15 ga watan Afrilu mai zuwa.

Idan baku manta ba, an samu tsaiko a Najeriya, har ta kai aka dage zabe ko soke shi a wasu yankuna daban-daban na kasar nan.

Kara karanta wannan

INEC Tayi Watsi da Kiraye-Kiraye, Ta Tsaida Ranar Rabawa Zababbun Gwamnoni Satifiket

INEC ta ce za a sake zabe a wasu yankunan Najeriya
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Mahmud Yakubu | Hoto; dailypost.ng
Asali: UGC

A wasu yankuna da jihohin a Najeriya, an samu tsaikon da ya kai ga zubar da jini, misali kamar jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da INEC ke cewa game da sake zabe a wasu yankuna

A sanarwar da INEC ta fitar a ranar Litinin 27 ga watan Maris, ta ce:

“A taron da ta gudanar a yau, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yanke shawarar cewa za a gudanar da dukkan zabukan gwamnoni, na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi da ba a yi ba a a ranar Asabar 15 ga Afrilu, 2023.”

Ya zuwa yanzu, hukumar bata bayyana sanarwar inda za a yi zaben ba a hukumance, amma ta ce za ta ba da bayani nan ba da jimawa ba.

INEC ta ayyana sakamakon zaben Adamawa ‘Inconclusive’

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

A wani labarin, kuma zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa, bata amince da sakamakon zaben jihar Adamawa da aka gabatar mata ba a makon da ya gabata.

Wannan ya faru ne sakamakon tsaiko da jinkirin da aka samu wajen tattara sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris da muke ciki.

Hukumar ta bayyana cewa, za a sake yin zaben a wasu yankunan jihar, inda ta bayyana cewa za ta sanar da lolacin bayan duba cikin tsanaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel