Jam’iyyar APC ta Kunshe Biliyoyin Kudi Wajen Saida Fam Ga Masu Sha’awar Takara

Jam’iyyar APC ta Kunshe Biliyoyin Kudi Wajen Saida Fam Ga Masu Sha’awar Takara

  • Za ayi sabon zaben Gwamna a jihar Kogi, wa’adin Yahaya Bello zai kare a farkon 2024
  • A jihohin Bayelsa da Imo, Hukumar INEC za ta shirya zaben Gwamna a karshen shekara
  • ‘Yan siyasa sun biya N50m wajen sayen fam naAPC da nufin shiga takara a Jihohin nan

Abuja - Maganar da ake yi, jam’iyyar APC ta samu abin da ya zarce Naira biliyan 1.3 ta hanyar saida fam ga masu sha’awar takarar Gwamna.

Za a yi zaben Gwamnoni a Kogi, Bayelsa da Imo a karshen shekara nan, Daily Trust ta ce jam’iyya mai mulki ta bude kofar saida fam a Fubrairu.

Duk wanda zai mallaki takardar nuna sha’awa da neman tsayawa takarar Gwamnan jiha zai biya Naira miliyan 50 zuwa ga asusun uwar jam’iyya.

Sakataren gudanarwa na APC na kasa, Suleiman Argungu ya fitar da jawabi cewa an saida fam din a sakatariyar daga 17 zuwa 22 na Fubrairu.

Kara karanta wannan

Yadda Rikicin 'Yan PDP da Gwamna a Arewa Suka Jawo Fasto Ya Ci Zaben Gwamna

Za a zabi sabon Gwamna a Kogi

A Kogi, masu neman zama Gwamna daga kowane bangare sun tanadi fam da niyyar cin gadon kujerar Gwamna Yahaya Bello da zai bar ofis a 2024.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu harin mulki a Jihar Kogi sun hada da Abdukareem Jamiu; Dr Sanusi Ohiare; James Faleke; Ahmed Ododo; Salami Deedat; da Shuaibu Audu.

Jam’iyyar APC
Shugabannin Jam'iyyar APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar ta ce sauran wadanda su ka kwallafa rai sun kunshi Yakubu Oseni; Akanta Janar na Jiha Momoh Jibril; Yusuf Okala da kuma Ashiru Idris.

Har ila yau akwai Halima Alfa, Stephen Ocheni, Abubakar Achimugu, Idachaba Friday, Salaudeen Abdulkudus, David Jimoh da Smart Adeyemi.

A karshe akwai Muritala Ajaka da mataimakin Gwamna Yahaya Bello watau Edward Onoja.

APC ta fara shirin zaben Bayelsa

A jihar Bayelsa, Timipre Sylva, Ogbomade Johnson, Joshua Maciver, da Barista Daumiebi Sunday Festus duk sun kashe kudi wajen sayen fam.

Kara karanta wannan

Shekarau da Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara 10 da 20 a Zaben Bana

Ragowar masu neman takarar su ne Farfesa Ongobi Maureen da Lyon Pereworimini David wanda ya yi nasara a 2019 kafin kotu ta soke zaben shi.

Idan aka koma Imo, jam’iyyar APC ce ta ke mulki don haka Hope Uzodimma zai nemi tazarce, Juliet Awa Obasi ce kurum ke neman ja da Gwamnan,

Shirin tsige Iyorchia Ayu a PDP

Rahotanni na nuna cewa ana kokarin fatattakar Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu daga ofishinsa yayin da abubuwan su ka cabe a NWC.

Majalisar NWC da ta ladabtar da wadanda suka yi zagon kasa amma ana fahimtar Ayu ba zai kubuta ba, za a iya yin kare jini-biri jini a rikicin PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel