Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar Dokoki Kan Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar Dokoki Kan Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Babbar Kotun tarayya mai zama a Yola ta tunɓuke dan majalisar dokokin Adamawa daga kan kujerarsa
  • Honorabul Musa Baroro, ya rasa kujerarsa ne bayan sauya sheka daga APC zuwa PDP bara
  • Bayan haka Alkalin Kotun ya yi watsi da karar da APC ta shigar da wasu yan majalisar tarayya biyu

Adamawa - Mamban majalisar dokokin jihar Adamawa, Honorabul Musa Baroro, ya rasa kujerarsa sakamakon sauya sheƙa daga jam'iyyar da ya ci zaɓe zuwa wata daban.

Baroro, wanda ya lashe zaben ɗan majalisar jiha karkashin inuwar APC a zaɓen 2019, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin Adamawa a watan Afrilu 2022.

Baroro.
Dan majalisar dokokin Adamawaz Musa Baroro Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto cewa sakamakon haka ne APC ta maka shi a gaban Kotu, ta roki mai shari'a ya ayyana kujerarsa a matsayin babu kowa.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban PDP Na Ƙasa Nan Take Kan Muhimmin Abu 1

Wane hukunci Kotun ta yanke?

Yayin yanke hukunci ranar Litinin, babbar Kotun tarayya ta umarci Honorabul Baroro, mai wakiltar mazaɓar Mubi ta kudu, ya sauka daga kan kujararsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Babbar Kotun tarayya mai lamba II da ke a Yola, babban birnin jihar Adamawa ta umarci ɗan majalisar jiha ya gaggauta barin kujerarsa nan take.

Kotun karƙashin jagorancin mai shari'a Saleh Kogo, ta yanke cewa ba zai yuwu Baroro ya fice daga APC zuwa PDP ba kuma ya ci gaba da zama kan muƙamin.

Alkali ya yi watsi da buƙatar APC

Bayan haka Mai shari'a Kogo ya yi watsi da ƙarar da APC ta shigar da mamba mai wakiltar mazaɓar Mubi ta kudu da mamba mai wakiltar Fufure/Gurin a majalisar wakilan tarayya.

Dukkan yan majalisar tarayyan guda biyu, APC ta kai ƙararsu ne kan sauya sheƙa zuwa PDP. Alƙalin ya ce APC ta gaza gamsar da Kotu da kwararan hujjoji.

Kara karanta wannan

Dani za a yi: Tsohon gwamnan jihar Arewa ya shiga jerin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa

Legit.ng Hausa ta gano cewa APC reshen Adamawa ta maka 'yan majasar uku a gaban Kotu ne kan sun koma PDP.

A wani labarin kuma Rikici Ya Tsananta, Kotu Ta Dakatar da Ayu Daga Bayyana Kansa a matsayin Shugaban PDP Na Kasa

Yayin da ake ta cece kuce kan makomar Iyorchia Ayu, wata babbar Kotu a Makurɗi ta haramta masa nuna kansa a matsayin shugaban jam'iyya na kasa.

Ta ba da wannan umarnin ne a karar da aka shigar gabanta daga jihar Benuwai, ta ɗage zaman zuwa watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel