Rikici Ya Tsananta: Kotu Ta Dakatar da Ayu Daga Matsayin Shugaban PDP Na Kasa

Rikici Ya Tsananta: Kotu Ta Dakatar da Ayu Daga Matsayin Shugaban PDP Na Kasa

  • Babbar Kotu mai zama a Makurdi ta umarci Iyorchia Ayu ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban PDP na ƙasa
  • Wannan na zuwa kwanaki kalilan bayan PDP reshen Jihar Benuwai ta dakatar da Ayu kan zargin cin amana da zagon ƙasa
  • Gwamna Wike ya dora laifin kayen da PDP ta sha a babban zaɓe kan Ayu, ya ce ya yi farin ciki da wannan ci gaban

Benue - Wata babbar Kotu mai zama a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai, ta dakatar da Dakta Iyorchia Ayu daga ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyar PDP na ƙasa.

Channels tv ta rahoto cewa Kotun ta yi wannan hanin ne har sai ta yanke hukuncin ƙarshe kan ƙarar dake gabanta, ta ɗage zamam sauraron karar zuwa 17 ga watan Afrilu, 2023.

Kara karanta wannan

Babbar Kotu Ta Kori Ɗan Majalisar Arewa Daga Mukaminsa Kan Muhimmin Abu 1

Iyorchia Ayu.
Shugaban PDP na ƙasa, Ayu Hoto: Iyorchia Ayu
Asali: Facebook

Wani mamban PDP daga jihar Benuwai, Terhide Utaan, wanda ya shigar da kara gaban mai shari'a W. I Kpochi, shi ne ya samu umarnin Kotu na haramtawa Ayu nuna kansa a matsayin shugaban PDP.

A makon da ya shige ne aka dakatar da Ayu kan zargin cin dunduniyar jam'iyya a lokacin da babbar jam'iyyar ke jimamin shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban PDP, Simon Imobo-Tswam, ya fitar ranar Litinin 27 ga watan Maris, ya ce shugabanni a matakin gunduma ba su da ikon dakatar da Ayu.

Babban abokin adawar Mista Ayu a cikin jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce ya yi farin ciki da shugabannin gunduma suka kaɗa kuri'ar rashin amincewa da shi.

A rahoton Vanguard, Wike ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Aike da Babban Saƙo Ga Tinubu, Ya Faɗi Faɗi Abinda Ya Kamata Ya Yi Wa Wike

"Ni ba dan jihar Benuwai bane amma na yi farin ciki kuma a yanzun jihar Benuwai ta gama mana komai, zamu iya fitowa mu faɗa wa duniya muna goyon bayan haka."

Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar Dokoki Kan Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

A wani labarin kuma Babbar Kotun tatayya ta kori ɗan majalisar dokokin jihar Adamawa kan sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Baya ga haka, Mai shari'a ya yanke cewa bai gamsu da hujjojin APC ba, don haka ya kori ƙarar da ta shigar da yan majalisun tarayya biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel