'Yan Najeriya Na Cikin Tsananin Yunwa da Fushi, Kungiyar Musulunci Ta Kokawa Tinubu

'Yan Najeriya Na Cikin Tsananin Yunwa da Fushi, Kungiyar Musulunci Ta Kokawa Tinubu

  • Yayin da fatara da yunwa ke ci gaba da fusata ‘yan Najeriya, kungiyar addini ta yi kira ga samo mafita cikin gaggawa
  • Imam Fuad Adeyemi ne ya yi bayyana bukatarsa ga Tinubu, inda yace ya kamata ya yaki fatara da yunwa idan ya karbi mulki
  • A cewarsa, ‘yan Najeriya na cikin matsanancin fushi da kuma azababben yunwa mara misaltuwa a wannan lokacin

FCT, Abuja - Kungiyar al’ummar Musulmi ta Al-Habibiyyah a ranar Lahadi ta bukaci zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a ranar Lahadi da ya mai da hankali kan yakar yunwa a kasar.

Hakazalika, kungiyar ta ce, ya kamata kuma shugaban ya mai da hankali ga yakar fatara da hauhawar farashin kayayyaki idan ya karbi ragamar kasar, jaridar Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Dena Ba Wa Mutanen Mu Gidan Haya Anambra, In Ji Miyetti Allah

Wannan kira na fitowa ne daga bakin babban limamin masallacin Al-Habibiyyah, Imam Fuad Adeyemi a wani taron da kungiyar ta shirya na hadin kai a Abuja cikin watan Ramadana.

An bukaci Tinubu ya yiwa yunwa da fatara yakin kare dangi a Najeriya
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasan Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, rahotannin Legit.ng Hausa a baya sun bayyana irin halin da ‘yan kasar nan ke ciki na ta’azzarar talauci da kuma karancin sabbin Naira a wannan shekarar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bukatar limamin ga Tinubu

Adeyemi ya bayyana bukatar cewa, ya kamata zababben shugaban ya tsaya tsayin daka wajen tafiyar da kasar daga ranar farko da ya karbi mulki.

Jaridar Vanguard ta naqalto Imam Adeyemi na cewa:

“Ko makaho yana gani kuma ko kurma na jin cewa akwai fatara a kasar; mutane na cikin yunwa kuma a fusace suke, tsadar kayayyaki kara hawa yake kuma a baya-bayan nan muka fara amfani da Naira wajen sayen Naira.

Kara karanta wannan

Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

“Yana bukatar yin aiki tukuru wajen kawar da wannan masifar. Nasarar Tinubu bata ba mu mamaki ba; sanannen fasihi ne kuma fitaccen shugaba mai tausayi.”

Za mu fatattaki yunwa da mayunwata a Najeriya a 2023

A wani labarin, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga manufofinsa a lokacin da yake kamfen, inda yace zai kawo karshen yunwa a kasar.

Tinubu ya yi wannan alkawarin ne a ziyararsa ta kamfen a jihar Adamawa, inda ya siffanta jam’iyyar PDP da jam’iyyar yunwa da mayunwata.

A cewarsa, gwamnatinsa za ta mai da hankali ne ga yin mulki don jin dadin al’umma da kuma kawo musu mafita ga matsalolinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel