Ina Goyon Bayan Dakatar da Shugaban PDP Na Kasa, Gwamna Wike

Ina Goyon Bayan Dakatar da Shugaban PDP Na Kasa, Gwamna Wike

  • Rigingimun da suka hana babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa watau PDP zaman lafiya sun kara daukar sabon salo bayan gama zaɓe
  • Hakan na zuwa ne bayan PDP reshen jihar Benuwai ta dakatar da shugaban jam'iya na ƙasa, Iyorchia Ayu, kan zargin cin amana
  • Da yake martani kan ci gaban, gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya goyi bayan matakin, ya ce Ayu na da hannu a faɗuwar PDP

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya maida martani kan dakatarwan da aka yi wa shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu.

Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa PDP reshen gundumar Igyorov, ƙaramar hukumar Gboko, jihar Benuwai, ta dakatar da Ayu a ranar Lahadi, 26 ga watan Maris, 2023.

Gwamna Wike da Ayu.
Gwamna Nyesom Wike da Iyorchia Ayu Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Kwamitin shugabannin PDP na gumdumar sun ɗauki wannan mataki ne bayan kaɗa kuri'ar rashin gamsuwa kansa bisa zargin zangon ƙasa da cin amanar jam'iya.

Kara karanta wannan

Tsoron Shiga Komar EFCC: Gwamna Wike Ya Bayyana Abinda Zai Yi Idan Ya Sauka Daga Mulki

Wike ya maida martani kan dakatar da Ayu

Da yake martani kan ci gaban yayin da ya bayyana a cikin shirin Channels tv mai suna Sunrise Daily, gwamna Wike ya nuna goyon bayansa ga matakin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya ce Ayu ya taka muhimmiyar rawa kuma ya yi ruwa ya yi tsaki wajen ganin an tumurmusa PDP ta ko ina a babban zaben 2023.

"Ina goyon bayan wannan dakatarwan da aka masa," Gwamna Wike ya ba da amsa lokacin da aka tambaye shi ko yana tare da matakin da PDP ta ɗauka a jihar Benuwai.

"Zancen gaskiya shi ne idan da shi (Ayu) ya bar kujerar da yake kafin yanzun, da fitowa zasu yi su ce ai saboda baya nan ne shiyasa PDP ta gaza kai bantenta a zaɓe."

Premium times ta rahoto cewa Ayu da Wike ba su ga maciji tun bayan ballewar gwamnonin PDP 5 waɗanda gwamnan Ribas ɗin ke jagoranta, sun nemi tilas ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugaban Jam’iyyar PDP Ayu Yayi Fatali da Dakatarwar da Akayi Masa

Ban dakatu ba - Ayu ya maida martani

A wani labarin kuma kun ji cewa Shugaban Jam’iyyar PDP Ayu Yayi Fatali da Dakatarwar da Aka yi Masa

Mai magana da yawun shugaban jam'iyyar PDP, ya bayyana cewa ko kaɗan Ayu bai dakatu ba saboda babu mai iya dakatar da shi sai NEC-PDP.

A wata sanarwa, Ayu ya ce kundin mulkin PDP ta tanadi masu alhakin dakatar da mamban NWC na ƙasa, wanda tsagin PDP da ya ce ya dakatar da shi bai san haka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel