Gwamna Umahi Ya Tona Asirin Ayu, Ya faɗi Yadda Ya Yi wa APC aiki a zaɓen 2023

Gwamna Umahi Ya Tona Asirin Ayu, Ya faɗi Yadda Ya Yi wa APC aiki a zaɓen 2023

  • Gwamna Umahi na jihar Ebonyi ya ce Ayu ya cancanci jinjina bisa aikin da ya yi wa Bola Tinubu a zaɓen 2023
  • Umahi yace rashin amince wa da batun murabus daga shugaban PDP ya taimaka soasai wajen baiwa APC nasara cikin sauki
  • Ya kuma yaba wa gwamna Wike bisa jajircewar da ya yi don tabbatar da adalci da daidaito a tsarin mulkin Najeriya

Rivers - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya ce shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya taimaka wajen nasarar jam'iyyar APC da Bola Tinubu a zaɓen shugaban kasan 2023.

Umahi ya faɗi haka ne ranar Litinin a jihar Ribas lokacin kaddamar da makarantar Sakandiren al'umma da aka sabunta a Okoro-nu-Odo, ƙaramar hukumar Obio-Akpor.

Gwamna Umahi tare da Wike.
Gwamna David Umahi tare da Wike a Ribas Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Umahi, babban bakon da Nyesom Wike ya gayyata, ya ce Ayu ya taimaka wa Tinubu da APC suka ci zaɓen shugaban kasa ta hanyar ƙin sauka daga shugaban PDP.

Gwamnan Ebonyi ya ce zai matuƙar wahala APC ta samu nasara da ace Ayu ya amince da buƙatar gwamnonin G-5 karkashin Wike, kamar yadda PM News ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa, Umahi ya ce:

"Ina ƙara gode wa dakataccen shugaban PDP na ƙasa, kun san ya taka rawa saboda inda ya amince ya yi murabus, da jam'iyyar APC ba zata ci zaɓe cikin sauki ba."
"Don haka, mutuminmu ne kuma na yaba da ƙwazonsa sosai. Bayan haka ina rokon Wike su cire takunkumin da suka sa masa saboda ya ci gaba da dakatar da ƙusoshi, mun son abinda yake aikatawa."
"Ina yaba masa (Ayu) sasai kuma ya zama wajibi ya sani cewa shi ya yi wa aiki a zaɓen da ya gabata."

A rahoton Vanguard, gwamnan Ebonyi ya yaba wa Wike wanda ya jajirce kan cewa kudancin Najeriya ya kamata su karbi mulki bayan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya gama wa'adinsa.

Yan Najeriya Zasu Yi Dokin Buhari Bayan Ya Sauka Daga Mulki, Shehu

A wani labarin kuma Mallam Garba Shehu yace nan gaba 'yan Najeriya zasu yi kewar shugaba Muhammadu Buhari bayan ya bar Ofis.

Kakakin shugaban kasan ya ce haka ta faru da tsohon shugaban kasa, Jonathan, yanzun mutane na kaunarsa kuma suna ganin girmansa.

Ya ce sai bayan Buhari ya miƙa mulki ranar 29 ga watan Mayu, sannan yan Najeriya zasu masa dawo dawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel