Siyasar Najeriya
Fitaccen lauya mai fafutukar kare hakkin ɗan adam, Festus Ogun, ya soki matakin shugaban ƙasa, Bola Tinubu bisa naɗa sabon gwamnan babban banki CBN.
Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Mista Lucky Aiyedatiwa, ya nesanta kanaa da wata takardar murabus da ake yaɗawa cewa ya yi murabus daga kan muƙaminsa.
Gwamnan jihar Filato, Celeb Muftwanga, ya naɗa masu taimaka masa na musamman 136 a faɗin kananan hukumomin jihar 17 kuma zasu soma aiki nan take.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya yi wasu yan sauye-sauyen wuraren aiki a cikin masu ba shi shawara ta musamman, waɗanda ya rantsar ranar Laraba.
Shugaban APC na kasa da tawagarsa ta NWC, gwamnoni da wasu kusoshin gwamnatin tarayya zasu ziyarci jihar Imo domin kaddamar da kwamitin kamfe ranar Asabar.
Jami'ar jihar Chicago daga ƙarshe ta saki kwafin takardun shaidar karatun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Hadimin shugaban ƙasar ne ya sanya su a Twitter.
Kotun koli da ake wa laƙabi da Kotun daga ke sai Allah ya isa ta kori ƙarar da jam'iyyar APC ta shigar tana kalubalantar nasarar gwamna Mbah na jihar Enugu.
A ranar 1 ga Oktoba Najeriya za ta cika shekara 63 da samun ‘yancin kai a hannun turawan Birtaniya. Kwamiti mai mutane 15 zai shirya bukukuwan da za ayi na bana.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya a jihar Oyo ta soke zaɓen dan majalisar jam'iyyar APC a mazaɓar Saki ta Yamma, ta umarci a sake.zaɓe.
Siyasar Najeriya
Samu kari