Kotu Ta Mayar Da Agballah a Matsayin Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Enugu

Kotu Ta Mayar Da Agballah a Matsayin Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Enugu

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta zartar da hukunci kan halastaccen shugaban jam'iyyar APC na jihar Enugu
  • Kotun tarayyar ta tabbtar da Barr Ugo Agballah a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar Enugu a yankin Kudu maso Gabas
  • Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar da ke ƙalubalantar nasarar Ugo a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar na jihar

Abuja - Babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja, ta yi fatali da ƙarar da ke ƙalubalantar zaɓen Barr Ugochukwu Agballah, a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, (APC) na jihar Enugu.

Kyaftin Orji Joseph Iloabanafor mai ritaya shine ya shigar da ƙarar mai lamba FHc/Abj/cv/57/2021 akan Agballah, jam'iyyar APC da hukumar shirya zaɓe ta ƙasa, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Peter Obi Ya Bayyana Zabinsa a Kujerar Shugabancin Majalisa

Kotu ta tabbatar da Ugo Agballah a matsayin shugaban APC a jihar Enugu
Ugo Agballah shugaban jam'iyyar APC na jihar Enugu Hoto: Dailypost.com
Asali: UGC

Maƙasudin shigar da ƙarar ta Orji shi ne yana ƙalubalantar zaman Agballah halastaccen ɗan jam'iyyar APC da kuma zaɓensa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar Enugu.

Orji ya buƙaci kotun da ta ayyana shi a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen ranar 16 ga watan Oktoban 2021, kuma zaɓaɓɓen shugaban jam'iyyar APC na jihar Enugu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ƙara ƙorafin cewa an amince shugaban jam'iyyar na jihar zai fito ne daga mazaɓar Aninri/Awgu/Orji River a wani taron ƙusoshin jam'iyyar da aka gudanar a ranar 15 ga watan Oktoban 2021 a ƙarƙashin jagorancin Sanata Ken Nnamani.

Kotun ta yi fatali da ƙarar

Da ya ke zartar da hukuncinsa a ranar Litinin da ta gabata, mai shari'a Emeka Nwite, ya amince da bayanin lauyan wanda ake ƙarar, Mr. T.M Ozioko Esq., na cewa rigingimun shugabancin jam'iyya a cikin gida ake sasanta su.

Kara karanta wannan

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe: Cikakken Jerin Jihohin Da Peter Obi Ke Kalubalantar Sakamakon INEC

Lauyan wanda ake ƙarar ya kuma tabbatar da Orji bai cika sharuɗɗan kundin tsarin mulkin jam'iyyar ba da zai yi takara a zaɓen wanda aka gudanar a shekarar 2021, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Hakan ya sanya alƙalin ya yi watsi da ƙarar da Mr Orji ya shigar a gabanta.

Bayan yanke hukuncin kotun, ta tabbata Ugochukwu Agballah zai ci gaba da zama halastaccen shugaban jam'iyyar APC na jihar Enugu.

Jigon APC Ya Nemi a Cafke Emefiele Da Ministocin Buhari

Rahoto ya zo kan yadda jigon jam'iyyar APC, Dr. Harun Garus Gololo, ya buƙaci hukmar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta binciki wasu jami'an gwamnatin da ta gabata.

Dr Haruna ya bayyana cewa ya shirya tursasa hukumar EFCC ta binciki tsohon ministan sufurin jiragen sama, Dr Hadi Sirika kan badaƙalar kafa jirgin saman Nigerian Air.

Asali: Legit.ng

Online view pixel