Gwamnan Jihar Filato Ya Dakatar da Wasu Ma'aikata Daga Bakin Aiki

Gwamnan Jihar Filato Ya Dakatar da Wasu Ma'aikata Daga Bakin Aiki

  • Gwamna Caleb Mutfwang, na jihar Filato ya soke wasu matakai da tsohon gwamna, Simon Lalong, ya ɗauka gabanin barin Ofis
  • A wata sanarwa da kakakin gwamna, Gyang Bere, ya fitar, ya ce gwamnan ya dakatar da ma'aikatan da aka ɗauka aiki tun 2022
  • Haka nan ya soke naɗin manyan sakatarori da kuma kara wa wasu ma'aikata wa'adin aiki bayan lokacin ritaya ya yi

Plateau - Gwamnan jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya, Caleb Mutfwang, ya dakatar da sabbin ma'aikatan da tsohuwar gwamnati ta ɗauka aiki daga 1 ga watan Oktoba, 2022 zuwa yau.

Sabon gwamnan na jam'iyyar PDP ya ce ba'a bi doka da matakan da aka saba ba yayin ɗaukar waɗannan ma'aikata da ya dakatar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan Filato.
Gwamnan Jihar Filato Ya Dakatar da Wasu Ma'aikata Daga Bakin Aiki Hoto: Caleb Mutfwang/facebook
Asali: Facebook

Daraktan hulɗa da jama'a da yaɗa labarai na mai girma gwamna, Gyang Bere, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

Gwamnan ya soke wasu naɗe-naɗen gwamnatin Lalong

Sanarwan ta ƙara da cewa gwamna ya umarci dukkan ma'aikata ko wasu mutane da tsohon gwamna ya naɗa a matsayin manyan sakatarori daga watan Janairu, 2023 su koma asalin muƙamansu na baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ruwayar jaridar Punch, sanarwan ta ce:

"Daga yau duk wasu ma'aikata da aka ɗauka aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2023 zuwa yanzu, mun dakatar da su daga aiki sai mun sake nazari kan hanyar da aka bi aka ɗauke su."
"Haka nan waɗanda suka aje aiki amman har yanzu basu bar Ofis ba saboda ƙara musu wa'adi ko basu aikin wucin gadi, su gaggauta miƙa kayan gwamnati da ke hannunsu kuma su bar aiki nan take."
"Bugu da ƙari duk ma'aikatan da lokacin aje aikinsu ya yi amma har yanzu basu miƙa takardar ritaya ba, su fara shiri tun yanzu su rubuta wasiƙar ritaya."

Kara karanta wannan

Iska Mai Ƙarfi Ta Yi Sanadin Rasa Rayyuka 2 Da Lalata Gidaje 20 a Jigawa

"Sannan duk ma'aikatan da aka naɗa a matsayin manyan Sakatarori daga watan Jamairu, 2023 zuwa yau su koma asalin wuraren da suke aiki a baya," inji sanarwan.

Gwamnan Enugu Ya Gana da Shugaba Tinubu, Ya Nemi Ya Sako Nnamdi Kanu

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Mbah na jihar Enugu ya faɗi wasu batutuwa da suka tattauna yayin ganawa da shugaban ƙasa a Abuja.

Ya ce daga ciki, ya roki shugaban ya duba yuwuwar sako shugaban ƙungiyar yan aware da aka ayyana da ta yan ta'adda IPOB..

Asali: Legit.ng

Online view pixel